Hajj 2019: Miliyoyin Musulmai na addu'o'i a filin Arfa

Tsayuwar Arfa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sama da Musulmi miliyan biyu da rabi ne suke tsayuwar Afra

Aikin hajji da musulmai kan yi a kowace shekara ya kai matuka a yau, inda mutane kimanin miliyan biyu da rabi suka taru a filin Arfa inda za su wuni suna addu'o'i tare da karatun alkur'ani.

Mahajjatan sun taru a kan wannan filin ne a gab da fitowar rana.

Wasu alhazan, musaman mata da tsofaffi da yara, da marasa lafiya kan fara tafiya filin na Arfa tun cikin daren takwas ga Zul-hajji.

Dole ne duk alhaji ya shiga filin Arfa kafin faduwar rana a ranar tara ga wata, duk wanda bai shiga filin ba kuwa to ya ba shi da wannan aikin hajjin, a cewar malamai.

Hukumomin Saudiya suna kai alhazai marasa lafiya a cikin motocin daukar marasa lafiya filin domin cika babban rukunin na aikin hajji.

Filin na Arfa na da nisan kimanin kilomita 15 daga birnin Makka.

A wannan fili ne dai annabi Muhammad (S.A.W) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, wadda ake kira hudubar ban-kwana.

Kuma ya yi hudubar ne a Masallacin Namira da ke filin na Arfa, sannan ya jagoranci musulmai suka yi sallar azahar da la'asar a hade.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masallacin Namira dake filin Arfa
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutane da dama na kokarin hawa dutsen Rahama da ake kira dutsen Arfa mai dimbin tarihi, to amma malami sun ce hawa dutsen ba shi da wani muhimmanci ga masu tsaiwar Arfa.

Aikin Hajji na daga cikin ginshikan Muslunci guda biyar, wanda ya wajaba musulmi mai hali ya aikata akalla sau daya a tsawon rayuwarsa.

Mahajjata dai na fitowa ne daga dukakkanin fadin duniya, to amma Indonesia wadda ita ce ta fi kowace kasa yawan Musulmai a duniya, ita ce ta fi kowace yawan Musulmai a wurin na aikin hajji.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daya daga cikin darussan da aikin hajji ke koyarwa shi ne karfafa dangantaka, da kuma nuna cewa kowane dan'adam daidai yake a gaban Allah madaukaki.

A lokacin aikin dukkanin alhazai maza kan sanya sutura iri wadda ake kira ihrami, yayin da su kuma mata kan sanya ko wane irin tufafi da suka ga dama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alhazai na dagewa da yin addu'a a ranar Arfa

Labarai masu alaka