Dubi abin da dauke wutar lantarki ya janyo a Burtaniya

King's Cross Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Yadda mutane suka yi cirko-cirko a filin jirgin kasa na King's Cross

Kamfanin da ke rarraba wutar ya ce akwai darussan da zai dauka sakamakon daukewar wutar da ya janyo mutum kusan miliyan daya suka shiga cikin duhu, a Ingila da Wales ranar Juma'a.

Darekata mai kula da ayyuka na kamfanin, Duncan Burt ya shaida wa BBC cewa injinan samar da wutar sun yi aiki yadda ya kamata, bayan da tashoshin bayar da wutar guda biyu suka samu tangarda.

Ya ce bai yadda cewa hari aka kai musu ta intanet ba, ko kuma a dora alhakin hakan ga rashin tabbas dangane da injinan samar da wuta daga iska ba.

Tuni dai kamfanin ya umarci a yi bincike dangane da hakikanin abin da ya faru.

Kamfanin ya ce zai dauki mataki dangane da abubuwan da suka biyo bayan daukewar wutar da suka hada da yadda fasinjoji suka rasa jirgin kasa da rincabewar yanayin ababan hawa sakamakon daukewar wutar da ke bayar da hannu da kuma yadda dubban mutane suka rasa wuta a gidajensu.

Har zuwa safiyar Asabar din nan dai wasu hanyoyin babu jiragen na kasa saboda rashin wutar.

Daukewar wutar dai ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma'a, inda kusan ilahirin yankunan Ingila da Wales suka kasance cikin duhu.

To sai dai wutar ta dawo a wasu sassan bayan minti 40 da kasancewa cikin duhu dundim.

Daya daga cikin manyan tashoshin jirgin kasa da ke birnin London, King's Cross na daya daga cikin wuraren da rashin wutar ya shafa matuka, inda aka kwashe awanni ba tare da jirgi ya tashi ko ya shiga tashar ba.

Hakkin mallakar hoto Timothy Choi
Image caption Bayanai dangane da tashi ko zuwan jirgin kasa sun dauke a tashar jirgin kasan ta Waterloo a London
Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Wasu fasinjojin da ke tsaye a wajen tashar jirgin kasa ta King's Cross bayan dauke wutar lantarki
Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Yadda wani ma'aikaci ya rinka yin amfani da cocilan wajen haska wa fasinjoji hanya tashar jirgin kasa ta Clapham Junction a London
Hakkin mallakar hoto James Marlow
Image caption Fasinjoji sun yi cirko-cirko a filin jirgin kasa
Hakkin mallakar hoto Lily Winnan
Image caption Nan kuma fasinjoji ne suka sauka daga jirgi inda suke tafiya a kafa sakamakon dauke wutar
Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Yadda aka rinka bai wa fasinjoji ruwan sha a tashar jirgin kasa ta Peterborough da ke London
Hakkin mallakar hoto Lily Winnan
Image caption Fasinjoji na tafiya a kasa bayan da jirgin ya tsaya sakamakon dauke wuta
Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Fasinjoji na fitowa daga tashoshin jirgin kasa na karkashin kasa a Clapham Junction station da ke London

Labarai masu alaka