Kazar PDP ta kyankyashe kwayayenta kaf a Bayelsa

BAYELSA Hakkin mallakar hoto Bayelsa State Min of Information and Orientation
Image caption Jam'iyyar PDP dai ba ta bar wa jam'iyyun adawa ko da kujera daya rak ba

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Bayelsan Najeriya ta lashe dukkannin kujerun shugabannin kananan hukumomi takwas da na kansiloli a zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar, a jihar Bayelsa.

Kafafen watsa labaran jihar sun rawaito cewa, masu zabe ba su fita rumfunan zabe ba yadda ya kamata duk da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Shugaban hukumar zaben jihar ta Bayelsa, Dr. Remember Ogbe ya shaida wa BBC Pidgin cewa an gudanar da zaben a kananan hukumomi takwas cikin lumana, irinsa na farko a tarihin jihar.

"Duk zaben da ya samu kaso 60 na fitar masu zabe, Allah ne kawai ya kiyaye kada kuri'a ba tare da rikici ba kuma babu wanda ya mutu, wannan abin godiya ne ga Allah."

Dr Ogbe ya kara da cewa jam'iyyu 44 daga cikin 91 suka shiga zaben to amma jam'iyyar adawa a jihar, APC na daga cikin jam'iyyun da ba su shiga zaben ba.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin shugaban jam'iyyar ta APC na jihar, Jotan Amos amma hakan bai samu ba.

Hakkin mallakar hoto Alambo Datonye
Image caption Shugaban hukumar ya ce jam'iyyu 44 ne suka shiga zaben

Karin bayani