Man Utd ta yi wa Chelsea cin kaca a wasan farko

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallon da Anthony Martial ya ci ce ta biyu a jerin kwallaye uku da Man Utd ta ci Chelsea

Kungiyar wasa ta Manchester United ta lallasa daya daga cikin masu adawa da ita wato Chelsea da ci 4-0, a wasan kungiyoyin na farko a kakar gasar Premier ta Ingila.

Yanzu haka Man Utd na da maki uku dai-dai da Manchester City, inda kuma take biye wa Man City a yawan gwala-gwalai.

Dan wasan Manchester United na gaba, Marcus Rashford ne ya fara tona wa ragar Chelsea asiri kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Anthony Martial ne ya sake daga ragar Chelsea a minti 65, kafin Marcus Rashford ya sake ganin zaran ragar Chelsea ya tsinka minti guda bayan ta Marshall.

Shi ma sabon dan wasan Man Utd, Daniel James ya wanke kansa ga 'yan kallo inda ya jefa kwallo ta hudu a ragar Chelsea.

Wannann dai ita ce nasara irinta ta farko da Manchester United ta taba samu a kan Chelsea a Old Trafford tun 1965.

Har wa yau, kwallayen hudu da Man Utd ta jefa a ragar Chelsea a tashin farko sun nuna irin gazawar kocin Chelsea, Frank Lampard a wasansa na farko na Premier League.

Maguire ya rike baya

Masu bibiyar harkar kwallon kafa da ma magoya bayan Manchester United sun ta zura ido domin ganin ko kwalliya za ta biya kudin sabulu dangane da sabon dan wasan baya da kungiyar ta saya a kan tsabar kudi har £80m, Harry Maguire.

Irin wasan da Maguire ya yi wajen kwace kwallo daga hannu dan wasan Chelsea, Tammy Abraham ya bai wa maras da kunya.

Hakan ne ya sa 'yan kallo magoya bayan kulob dinsa suka yi ta sowa.

Irin nutsuwarsa a lokacin tashin hankali domin kare gidansa a duk lokacin da baraka ta afku ya kayatar da masoya.

Maguire ba ya harba-ta-mati wajen karbar kwallo da rabawa da kuma duba abokan wasan lokacin da ya kamata ya mika kwallo a gare su musamman Paul Pogba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harry Maguire dan wasan da Man Utd ta saya a kan £80m
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marcus Rashford

Labarai masu alaka