'Yan awaren Yemen sun kwace birnin Aden

Aden has been the temporary base of President Abdrabbuh Mansour Hadi's government Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Aden ne shalkawatar Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi da dakarun da ke masa biyayya

Gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake gwambzawa a Yemen ta gargadi 'yan awaren kasar da su janye daga birnin Aden.

'Yan awaren sun kwace birnin ne ranar Lahadi daga mayaka masu biyayya ga shugaban kasar Abd-Rabbuh Mansour Hadi.

Rikicin yayi kamari har ya kai ga matsayin da wasu na ganin akwai yiwuwar yakin na Yemen zai kara kazancewa.

A halin yanzu akwai alamar cewa babu wani sabon yaki a birnin na Aden.

Fadan da ya barke na baya-baya nan ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 40, inda kuma daruruwa suka sami raunuka.

'Yan aware da dakarun gamayyar Saudiyyar sun amince da a tsagaita wuta, matakin da kawo yanzu babu wanda ya taka shi duk da wani hari da Saudiyyar ke kai wa da jiragen yaki kan wani sansanin 'yan awaren a arewacin birnin.

Amma akwai damuwa wannan shirin ba zai dore ba, domin 'yan awaren sun yi watsi da wata bukata ta su janye daga birnin da suka kwace, wanda a cikinsa akwai fadar shugaban kasar.

Akwai lalamar cewa danagantaka tsakanin kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya za ta iya kara tabarbarewa.

A bangare daya, Saudiyya ta na goyon bayan Shugaba Abd-Rabbuh Mansour Hadi, wanda a yawancin lokuta ke zaune a Riyadh inda yake gudu hijira.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa ba sa ganin shugaban zai iya jagorantar kasar ta Yemen.

Ga shi yanzu lamarin ya jagule, kuma babu wani bangare da zai iya kawo karshen wannan yakin.

Labarai masu alaka