Madrid na son Neymar, AC Milan da Roma na zawarcin Lovren

PSG forward Neymar in training Hakkin mallakar hoto Getty Images

An wallafa wasu hotuna da ke nuna lauyoyin Paris St-Germain da na Neymar na Brazil mai shekara 27, sun shiga ofishin Barcelona. (Gol TV, via AS)

Har yanzu Real Madrid na sha'awar karbo Neymar, kuma za ta daina farautar dan wasan Manchester United Paul Pogba idan har ta karbo shi. (Sun)

Wasu alamu sun nuna PSG ta dakatar da sayar da rigar Neymar a kantinanta. (UOL Esporte, via Marca)

Gareth Bale, mai shekara 30, ya shirya wa rayuwa a benci a Real Madrid har zuwa sake bude kakar wasa domin komawa China a watan nuwamba ko kuma idan an kori Zinedine Zidane. (Mail)

Manchester United na cike da mamakin yadda Pogba ya nuna cewa har yanzu zai iya barin kungiyar a wannan lokacin. (Mirror)

Bayern Munich na tattaunawa da Barcelona game da aron Philippe Coutinho, mai shekara 27, tare da fatan sayen dan wasan a karshen kaka. (RAC1, via AS)

Bayern Munich ta diba lafiyar dan wasan da Inter Milan Ivan Perisic wanda take shirin kammala karbar aronsa da nufin sayensa a badi. (Bild - in German)

Juventus ta tuntubi dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, domin karbar aronsa idan kwantaraginsa da Tottenham ta kawo karshe a karshen kaka. (Mail)

A wannan makon ake sa ran dan wasan Liverpool Daniel Sturridge, mai shekara 29, zai yanke shawara kan makomarsa, inda kungiyoyi 13 ke bukatarsa, cikinsu har da tayin Fenerbahce na £60,000 duk mako. (Telegraph)

Liverpool za ta amince da tayin Fam miliyan 15 kan Dejan Lovren wanda AC Milan da Roma suka nuna sha'awar suna so. (Liverpool Echo)

Kungiyar David Beckham ta Amurka Inter Miami ta nuna sha'awar dan wasan Uruguay Edinson Cavani, 32, idan har kwangilar shi ta kare a PSG a 2020. (Fox Deportes - in Spanish)

Labarai masu alaka