BBNaija: 'Yar sandar Birtaniya ta fito a shirin talabijin ba tare da izini ba

Khafi Kareem Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta ce Khafi ba ta samu izini ba kafin fitowa a shirin Big Brother Naija

Wata 'yar sandar birnin Landan tana ci gaba da fitowa a shirin talabijin na Big Brother Naija a tashar Africa Magic duk da cewa ba ta samu amincewar yin hakan ba.

Rundunar 'yan sandan birnin Landan ta ce ta kaddamar da wani binciken kan batun a cikin gida bayan 'yar sandar mai suna Khafi Kareem ta bayyana a shirin, ba tare da "an ba ta izinin yin hakan ba".

Hedkwatar 'yan sandan birnin Landan ta ce Khafi, mai shekara 29 wadda 'yar Najeriya ce, ta karbi dogon hutu ne daga wurin aiki "bisa wani dalili na daban".

Wani da yake magana da yawunta ya ce "za ta yi magana kan batun idan lokaci ya yi."

Tashar talabijin ta Africa Magic ta ce Khafi ta shiga shirin ne "don amfanin zamantakewa".

An wallafa wani bayani a shafin tashar wanda yake cewa Khafi za ta kashe kyautar naira miliyan 30 (kimanin fan 68,000) wajen yin wani shirin tafiye-tafiye a Najeriya da wasu ayyukan agaji.

Hakkin mallakar hoto The Metropolitan Police
Image caption Khafi Kareem ta taba daukar hoto tare da Kwamishinar 'yan sanda Cressida Dick lokacin da aka cika shekara 100 da fara sanya mata a aikin tsaro

Rundunar 'yan sandan ta ce Khafi ta samu izinin tafiya dogon hutu ne amma ba a amince mata ta bayyana a shirin talabijin din ba.

"Rundunar tana sane cewa 'yar sandan ta bayyana a shirin ba tare da izini ba.

"Rundunar ta ce ba ta goyon bayan bayyanar 'yar sandar a shirin kuma ba ta wakiltar rundunar."

A karshe ta ce duk wani jami'inta da aka samu laifin saba ka'idojin aiki zai iya fuskartar hukunci.

Labarai masu alaka