Najeriya na yunkurin hana shiga da abincin waje kasar

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muhammadu Buhari ya yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar wanda ya shiga halin La-haula a wa'adin mulkinsa na farko

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin kasar da ya daina bai wa masu shigo da abinci kasar kudaden kasar waje a wani mataki na bunkasa harkar noma.

Ya ce kamata ya yi a adana kudaden da ke asusun kasar na kasashen ketare domin amfani da su wurin fadada tattalin arzikin kasar "maimakon daure wa masu shigo da abinci daga kasashen waje gindi."

"Ka da ku bayar da ko taro ga mutanen da ke son shigo da abinci kasar nan," kamar yadda mai magana da yawunsa ya ambato shi yana cewa a lokacin wani taro da wasu gwamnonin kasar a mahaifarsa ta Daura ranar Talata.

Tattalin arzikin Najeriya shi ne mafi girma a nahiyar Afirka amma tana shigo da abinci mai yawa daga kasashen ketare domin ciyar da jama'arta.

Shugaba Buhari, wanda ya lashe zabe karo na biyu a farkon bana, ya yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda ya shiga halin La-haula a wa'adin mulkinsa na farko.

Najeriya ce kasar da ta fi kowacce hako danyen mai a Afirka kuma kudaden da ke fitowa daga fannin su ne kashin-bayan tattalin arzikinta.

Sai dai kaso mai tsoka na tafiya ne a tallafin shigo da abinci da sauran kayan bukata na yau da kullum da kuma manyan injina.

Hukumar Kididdiga ta kasar (NBC), ta ce a watanni ukun farko na bara, kasar ta kashe dala miliyan 503 wurin shigo da kayan abinci. Sai dai wannan adadin ya karu da kashi 25.84 a watanni ukun farko na bana.

A wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya dakatar da shiga da shinkafa ta iyakokin kasar na tudu da kuma hana masu shigo da ita samun kudaden kasashen waje daga gwamnati.

Matakin dai wani yunkuri ne na bunkasa noma a kasar, sai dai kuma hakan ya sa kasuwar masu fasa-kwauri ta bude a wasu iyakokin kasar.

Makwanni biyu da suka wuce ma babban bankin ya daina sayar wa da masu shigo da madara da sauran nau'ikanta kudaden waje, yana mai cewa akwai bukatar a bunkasa kamfanonin da ke samar da ita a cikin gida.

Bankin dai yana zaman kansa ne, a don haka za a zuba ido a ga yadda zai tunkari umarnin shugaban.

Idan har ya amince da umarnin, to akwai yiwuwar farashin abinci ya karu saboda masu shigo da shi za su koma sayen kudaden waje a kasuwannin bayan fage, inda suke da tsada fiye da farashin hukuma.

Wasu 'yan Najeriya da dama sun dora alhakin matsin tattalin arzikin da aka samu a wa'adin farko na shugaban kan wasu matakai da ya dauka da suka shafi kasuwar musayar kudi.

Sai dai wasu sun yaba masa suna masu cewa ta haka ne kawai za a bunkasa kamfanoni da kuma karfafa gwiwar 'yan kasuwa na cikin gida.

Labarai masu alaka