Hira da diyar Sheik Ibrahim Zakzaky
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Halin da mahaifana suka shiga a Indiya - Suhaila Zakzaky

Latsa alamar lasifika domin saurarar cikakkiyar hira da Suhaila Zakzaky.

Bayanai daga kasar Indiya na nuna cewa an samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Sheikh Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa bayan da suka isa kasar domin duba lafiyarsa.

Daya daga cikin 'ya'yansa Suhaila ta shaida wa BBC cewa "ba a barsu sun ga likitocin da suka zaba su gani ba tun farko, kuma shugabannin asibitin sun ce su ne za su zaba musu likitoci", lamarin da ta ce ya sa har yanzu "ba a fara yi musu magani ba".

Ta kara da cewa "ana tsare da mahaifan nata a wani yanayi mai tsanani".

Kalaman nata sun yi kama da wadanda ke kunshe a wata murya da ke yawo a shafukan sada zumunta wadda aka ce Zakzaky ne da kansa yake korafi kan yadda ake tsare shi.

Wasu majiyoyi sun ce gwamnatin kasar ta Indiya ta ba malamin wani wa'adi na ya koma Najeriya idan bai amince da likitocin da aka ba shi ba, sai dai Suhaila ta ce har yanzu bai yanke shawara kan hakan ba.

Sai dai kawo yanzu hukumomin asibitin, wanda shi Zakzaky ne da kansa ya zabi zuwa can, ba su ce komai ba kan wadannan zarge-zarge.

Amma kafar yada labarai ta PRNigeria ta ce ta samu bayanan da ke cewa an cimma matsaya kuma yanzu malamin ya yarda a duba shi bayan da asibitin ya amince masa ya ga likitocin da yake so.

Labarai masu alaka