Yadda masu garkuwa suka sace fasto da dansa a jihar Kaduna

Sifeton 'yan sanda Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Sufeton 'yan sanda

Rahotanni dai sun ce masu garkuwar sanye da kayan sojoji su 20 sun kutsa gidan faston da ke unguwar Makere da ke yankin karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Al'amarin ya faru ne da misalin karfe biyu na daren Talata, inda suka yi amfani da karfi suka yi awon gaba da fasto Elisha da dansa mai suna Emmanuel.

To sai dai daga baya masu garkuwar sun saki dan faston "domin ya zama tsani tsakanin masu garkuwar da iyalan faston."

Shugaban kungiyar Kiristoci na jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab ya ce masu gaskuwar sun nemi naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.

Rabaran Hayab ya ce akalla a baya-bayan nan an sace fasto-fasto guda uku a jihar, sannan an sace Kiristoci fiye da 100, inda ya ce a tsawon shekaru biyu Kiristoci sun biya naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa.

Batun garkuwa da jama'a dai na karuwa a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Karanta wasu karin labarai:

Labarai masu alaka