Yadda ziyarar Shugaban Guinea ta hada Ganduje da Sarki Sanusi

A Hakkin mallakar hoto Muhd Kano Emirate
Image caption A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano

Mako biyu gabanin babbar sallah, idan aka ce Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II za su hadu a lokacin bukukuwan sallah fiye da sau biyu, mutane da dama za su yi mamaki, wasu ma za su yi watsi da maganar a matsayin yasasshen zance.

An yi zaton za a sake komawa ruwa, a sake shata layi tsakanin bangarorin biyu a cikin makon sallah, lokacin da masarautar Kano ta aike wa duka hakimai takardar cewa su kai dawakinsu Kano domin yin hawa.

Sai dai gwamnatin jihar ba ta yi wata-wata ba wajen fitar da wata sanarwa tana umartar duka hakiman jihar su tafi sababbin masarautunsu su yi hawan sallah a can, wanda hakan a fili mataki ne na kalubalanatar umurnin masarautar Kano.

A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Hakkin mallakar hoto DG Media KN
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II lokacin da yake jagorantar sallar idi a Kano ranar Lahadi

Gwamnati ta ce an kirkiro sababbin masarautun ne domin tabbatar da ci gaba, to amma wasu majiyoyi na kusa da gwamnati sun ce tana son daukan fansa ne kan rashin goyon bayan da ake zargin Sarki Saunsi bai ba wa Ganduje ba a yayin zaben shekarar 2019, wanda Gandujen ya nemi takara a karo na biyu.

Dangantaka ta ci gaba da yin tsami har zuwa watan Yuni, kafin wasu manya a Najeriya su saka baki da nufin sasanta manyan mutanen biyu na Kano.

Rashin kyawun dangantakar ta sa gwamnati soke hawan karamar sallah da Sarkin Kano ke yi, sai dai an yi hawan a sababbin masarautun Karaye da Rano da Gaya da kuma Bichi da gwamnatin Gaduje ta kirkiro.

Abin da ya sa wasu ke ganin kamar bita-da-kulli ake yi wa Sarki Sanusi.

A lokacin hawan na karamar sallah dai manyan jam'ian gwamnati sun je kallon hawa a sabbin masarautun a matsayin manyan baki, sai dai babu wanda ya je kallon hawan Sarki Sanusi da sunan gwamnatin Kano.

Daga baya dai wasu manyan mutane da suka hada da Alhaji Aliko Dangote da shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi sun shiga tsakani inda suka yi wani zaman sulhu tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano.

Abin da ake ganin ya taimaka wajen yayyafa wa kurar da ta taso ruwa.

Hakkin mallakar hoto Muhd Kano Emirate

Duk da cewa an dan samu sassauci kan bayyanar sabani tsakanin sarki da gwamna, an ci gaba da zaman 'yan marina tsakaninsu, inda kowa yake harkarsa ba tare da shigar da dayan ba.

Mutane da dama sun zaci rigima za ta sake komawa sabuwa, bayan masarautar Kano ta aikewa hakima wasika cewa su halarci hawan sallah a Kano, yayin da ita kuma gwamnati ta fitar da sanarwa tana umartar kowane hakimi ya yi sallah a masarautar da yankinsa ta fada.

To sai dai a iya cewa abubuwan da suka faru sun bai wa kowa mamaki, ganin yadda gwamnan da sarkin Kano suka hadu sau shida daga ranar Lahadi da aka yi sallah, zuwa ranar Talata da aka yi hawan Nasarawa.

A kowace rana dai manyan mutanen sun hadu sau biyu a wurare da lokuta daban-daban, abin da ba wanda ya taba zaton hakan zai faru a nan kusa.

Haduwa ta farko ita ce wacce suka yi a filin idi, inda fuskokin shugabannin biyu suke cike da annashuwa fiye da yadda suka hadu a lokacin karamar sallah lokacin da ake tsaka da rikici tsakaninsu, inda fuskokinsu suke nuna alamun ta-ciki na ciki.

Haduwa ta biyu ita ce wacce gwamna ya kai wa sarki ziyarar barka da sallah ta al'ada, inda shugabannin suke haduwa a gidan Shatima kusa da fadar Sarkin Kano.

Da karamar sallah dai gwamnan bai kai irin wannan ziyara ba, kasancewar duka bangarorin na ciki da juna.

Haduwa ta uku ita ce wadda gwamnan tare da Shugaban kasar Guinea Bissau Alpha Conde suka kai ziyara fadar Sarkin Kano kallon hawan Daushe na Sarkin Kano a ranar Litinin.

A karamar Sallah dai gwamnan Kano ya aikewa Sarkin Kano takarda cewa ba zai je kallon hawan ba, saboda wasu al'amura da suka sha gabansa, to amma gwamnan ya je kallon makamancin wannan hawa a sabuwar masarautar Bichi.

Hakkin mallakar hoto Muhd Kano Emirate

Haduwa ta hudu ita ce a daren Litinin din, inda Sarkin Kano ya kai ziyara fadar gwamnati karon farko cikin watanni kuma karon farko da suka hadu da gwamna a gidan gwamnati tun bayan zaben watan Maris.

Sarkin dai ya je cin abincin dare ne da aka shirya wa Shugaba Conde.

Da safiyar Talata kuma Sarkin Kano ya kai wata ziyarar ta al'ada gidan gwamnati yayin kasaitaccen hawan Nasarawa, wanda a karamar sallah gwamnati ta ce ta soke hawan saboda abin da ta ce dalilan tsaro.

Hakazalika da yammacin Talatar sarkin ya koma gidan gwamnati, inda aka yi wani taron cinikayya da Shugaban Conde, inda sarkin ya yi jawabi na musamman a wajen.

Tun bayan zuwan Turawa ne aka fara hawan Nasarawa, inda sarki ke kai ziyarar jaddada mubaya'a ga gwamna, sannan su yi jawabai kan al'amuran da suka shafi al'umma.

A yayin hawan, Sarkin Kano ya ce zai ci gaba da bai wa gwamnatoci hadin kai, sannan ya yi kira ga jama'a su ci gaba da bai wa gwamnatoci goyon bayan kan abubuwan da suka shafi ci gaban al'umma.

Shi ma da yake mayar da jawabi, gwamnan Kano ya yi nuni da tamkar babu wata matsala tsakanin bangarorin biyu.

A yayin jawabin dai babu inda gwamnan ya ambaci sabbin masarautun jihar, haka kuma ba a ga ko da daya daga sauran sarakunan na Kano masu daraja ta daya a wajen hawan ba.

Sai dai shi ma sarkin na Kano ya kauce wa duk wata magana da za ta nuna akwai sabani tsakanin bangarorin biyu.

Tasirin ziyarar Alpha Conde

Hakkin mallakar hoto Kano Emirate
Image caption A cikin haduwa shida da gwamna da sarkin Kano suka yi, hudu daga ciki sun yi ne tare da Shugaban Guinea.

An shafe kimanin wata uku ba a ga-maciji tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano, kuma duka bangarorin biyu sun rinka kauce wa haduwa da juna, ko kuma a ce babu wani dalili da ya sa shugabannin biyu suka hadu da juna a tsawon lokacin.

A cikin haduwa shida da gwamna da sarkin Kano suka yi, hudu daga ciki sun yi ne tare da Shugaban Guinea.

Mai yiyuwa ba domin ziyarar da ya kai Kano a lokacin na sallah ba, da watakila sau daya ko sau biyu kawai za su iya haduwa.

Wasu na ganin sarkin da gwamna sun yi kokari ne su ajiye duk wani sabani da ke tsakaninsu, sannan su samu damar haduwa da shugaban kasar Guinea a lokuta daban-daban domin kulla alaka tsakaninsu ko kuma inganta ta.

Wasu kuma na ganin sarkin da gwamna sun ajiye sabanin da ke tsakaninsu ne domin girmama bakon Shugaba Buhari, kasancewar shugaban Guinea ya fara yada zango ne a Daura, inda ya yi sallah a can, ya kalli hawan ranar sallah a masarautar Daura.

Idan da Sarkin Kano da gwamna sun bari sabanin da ke tsakaninsu ya yi tasiri har ya hana daya daga cikinsu halartar daya daga ganawar da aka yi da shugaban Guinea, hakan zai iya zama wani abin kunya ga Najeriya ta fuskar diflomasiyya, a cewar wasu masu sharhi.

To amma babban abin da wasu suka lura da shi, shi ne shugaban Guinea ya taka muhimmiyar rawa wajen kusanto da shugabannin da ba sa ga maciji kusa da juna, abin da aka rasa wani mutum daya da zai yi hakan a shugabannin Najeriya a baya.

Akwai sauran rina a kaba

A lokacin da sarki ya je ziyarar Hawan Nasarawa fadar gwamnati, hakimansa da dama sun take masa baya.

Kuma cikin wadanda suka rufa wa sarkin baya akwai hakiman da aka dakatar da su a wasu masarautun saboda sun ki komawa can din su yi hawa tare da sababbin sarakuna, inda suka gwammace su ci gaba da zama da sarkin Kano a matsayin hakimansa, ko da kuwa za su rabu da kasar da suke hakimci.

Hakimai 16 ne dai wannan lamari ya shafa, da suka hada da duka masu zaben sarkin Kano, da sauran manyan hakimai a masarautar Kano.

Wasu na ganin gwamnati za ta iya daukan mataki a kansu, amma wasu kuma na ganin iya abin da gwamnati za ta iya yi shi ne raba su da garin da suke hakimci, da dakatar da albashinsu, abin da kuma ba lalle ya yi tasiri a kansu ba.

Sai dai wasu na ganin zai yi wahala gwamnatin ta dauki wani mataki a kansu, kasancewar batun kirkirar masarautun yana gaban kotu, a shari'ar da masu zaben sarki suka shigar da karar gwamnatin Kano suna kalubalantar kirkirar sabbin masarautu a Kano.

Wasu daga cikin hakiman dai sun yi hawa tare da sarkin Kano kuma sun bi shi gidan gwamnati, yayin da wasu kuma wakilansu ne suka yi hawan tare da sarkin Kano.

Hakiman da suka bijire wa gwamnatin Kano

1.Madakin Kano hakimin Dawakin Tofa (Shugaban masu zaben sarkin Kano)

2.Makaman Kano hakimin Wudil (Mai zaben sarkin Kano)

3.Sarkin Dawaki mai Tuta hakimin Gabasawa (Mai zaben sarkin Kano)

4.Sarkin Bai hakimin Dambatta (Mai zaben sarkin Kano)

5.Matawallen Kano hakimin Minjibir

6.Sarkin Shanu hakimin Rimin Gado

7.Dan Amar hakimin Doguwa

8.Yariman Kano hakimin Takai

9.Sarkin Fulanin Ja'idanawa hakimin Garun Malam

10.Dan Madami hakimin Kiru

11.Dan Galadima hakimin Bebeji

12.Barden Kano hakimin Bichi

13.Dan Isan Kano hakimin Warawa

14.Dokajin Kano hakimin Garko

15.Dan iyan Kudu hakimin Dawakin Kudu

16.Dan Makwayon Kano hakimin Tsanyawa

Labarai masu alaka