Fargabar tattalin arzikin duniya ta sa faduwar hannayen jari

Jami'i a kasuwar hannun jari ta Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fargabar tattalin arziki a duniya ce ta sa hannayen jari faduwa a kasashe

Kasuwar hannayen jari a kasashen duniya daban-daban musamman masu karfin tattalin arziki ta fadi sakamakon fargabar da ake yi ta shiga matsalar tattalin arziki a duniya.

Farashi a kasuwannin kasashen Asiya sun yi kasa sosai, a ranar Laraba, bayan da rahotanni suka nuna cewa manyan kasuwannin hannun jari na Amurka sun rufe, a farashi kasa da kashi uku cikin dari.

Wannan shi ne karon farko tun watan Oktoba na shekarar da ta wuce, 2018, da farashi a manyan kasuwannin hannun jarin na Amurka, wato Dow Jones, ya yi faduwa mafi girma a rana daya.

Wannan dai ya faru ne bayan da masu zuba jari a gwamnatin Amurka suka zabi takardun lamuni na tsawon wa'adi, saboda fargabar da suke da ita game da yanayin tattalin arzikin kasar.

A wani bincike da BBC ta yi ta gano cewa wani abu kuma da ke tayar da hankalin masu zuba jari shi ne, alkaluman tattalin arziki marassa karfafa guiwa da ake samu daga kasashe biyu masu karfin arziki.

Inda tattalin arzikin Jamus ya ragu a wata uku da suka gabata, sannan ayyukan samar da kayayyaki a masana'antun China na raguwa.

Wannan ne ma ya sa masu hada-hadar hannun jari ke ta kokarin karkata ga sayen abubuwan da ba za su kai su ga asara ba, musamman takardun lamuni da gwal.

Uwa-uba kuma abin da ke kara jefa tattalin arzkin na duniya cikin halin kaka-ni-kayi shi ne rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China, kamar yadda binciken na BBC ya nuna.

Haka kuma yanayin ya sa Shugaba Trump ya sa babban bankin Amurka cikin karin matsin-lamba, kan cewa bankin ba ya yin abin da ya kai ya yi na tallafa wa tattalin arzikin kasar, mafi karfin arziki a duniya.

Ana ganin matsin na Mista Trump a kan babban bankin Amurkar zai iya kawar da kwarin guiwar masu zuba jari a kan bankin su ga cewa bankin ba zai iya daukar hukunci na kashin kansa ba.

Mai sharhi kan al'amuran tattalin arziki da kasuwanci Oliver Pursche, daga kamfanin hada-hadar kudade na Bruderman, ya ce yanayin tattalin arzikin na duniya na da ban tsoro.

Ya ce: ''Meyake faruwa a Homg Kong, me yake faruwa da shirin ficewar Birtaniya daga Turai, da kuma rigimar tattalin arziki tsakanin Amurka da China, dukkanninsu hadari ne,''

Masanin ya kara da cewa:'' Kowa ne babban banki a duniya yana kokarin bunkasa tattalin arzikin kasarsa, kuma kowa ne dan siyasa a kasarsa a fadin duniyar nan na kokarin lalata tattalin arzikin kasar ne.''