Ibrahim Zakzaky ya so bijirewa a Indiya – Gwamnatin Najeriya

Zakzaky ya kwashe shekara hudu a tsare a hannun hukumomin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce Sheikh Ibrahim Zakzaky ya so a ba shi damar yin abubuwa da suka saba wa ka'idojin tafiyarsa.

A cikin wata murya da aka rinka yadawa ta kafafen sada zumunta, ta ambato wani da aka yi ikirarin Shiekh Ibrahim el-Zakzaky ne na cewa an masa takurar da bai taba ganin irin ta ba, a wani asibiti da ke kasar Indiya.

Sai dai sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta hannu babbar sakatariyar ma'aikatar yada labarun kasar Grace Isu Gekpe, ta ce "ya kamata a yi watsi da ikirarin da yake yi (El-Zakzaky) na cewa ana tsare da shi a yanayin mai muni fiye da yadda yake tsare a Najeriya".

Sanarwar ta ce shugaban na kungiyar IMN, ya nemi da a ba shi wasu damammaki a sa'ailin tafiyar tasa, wadanda aka hana domin ba su cikin tsarin tafiyar tasa.

Wadannan abubuwa kuwa sun hada da, barin likitoci wadanda shi ne kawai ya amince da su su duba shi, da mika masa fasfo dinsa a lokacin da suka isa Dubai, da ba shi damar zama a otal a maimakon asibiti, da kuma bukatar a janye 'yan sanda da ke tsaron shi a kasar ta Indiya.

Zargin da malamin na Shi'a ya yi a cikin muryar da aka yada ya janyo hankalin mabiya akidar ta harkar Islamiyya a Najeriya, inda suka yi zargin cewa da hadin bakin gwamnatin Najeriya ne ake takura wa mallam Zakzaky, wanda ya je neman magani a kasar ta Indiya bayan samun sahhalewar kotu.

A wata hira da ta yi da BBC, diyar Sheikh Ibrahim Zakzaky mai suna Suhaila ta tabbatar da cewa mahaifin nata ya koka game da yanayin da ake tsare da shi a kasar ta Indiya.

Sai dai a yanzu bayanai sun nuna cewa an samu matsaya game da yadda likitoci za su rinka bai wa malamin kulawa, inda ake sa ran za a ci gaba da duba lafiyarsa.

A ranar 12 ga watan Agusta ne dai el-Zakzaky da mai-dakinsa Zeenat suka tafi Indiya domin neman magani, bayan kwashe shekaru ana tsare da su.

Tsarewar da gwamnatin Najeriya ta yi masa ta janyo jerin zanga-zanga daga magoya bayansa, abin da ya haifar da rasa rayuka.

A ranar 5 ga watan Agusta ne wata babbar kotu da ke Kaduna ta bai wa Sheikh Zakzaky damar zuwa neman magani a kasashen ketare, bayan kai-ruwa rana da aka yi ta yi a kotu a wata shari'a da ake yi tsakanin sa da gwamnatin jihar Kaduna.

Labarai masu alaka