An kama dan sandan da ya ce 'zai kai wa sojoji hari'

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto others
Image caption Kisan 'yan sandan da sojin suka yi ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar

An kama wani dan sandan Najeriya bayan da ya wallafa wasu bayanai a shafin Facebook da ke barazar cewa zai dauki fansa kan kisan da sojoji suka yi wa wasu abokanan aikinsa.

Wani kwamishinan 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa ana tsare da Sunday Japhet a jihar Bauchi kuma "za a ladabtar da shi".

A makon da ya gabata ne, sojoji suka kashe wasu 'yan sanda uku da kuma farar hula guda a jihar Taraba bayan da suka bude wuta kan wata motar bas wacce 'yan sandan suka dauko wani mai laifi a ciki.

Sojoji sun ce sun yi amannar cewa akwai masu satar mutane a motar.

Mista Japhet ya fada a Facebook cewa: "Ba zai yi wu a kashe wadannan ['yan sandan ba] haka kawai, kuma a bar iyalansu a cikin kunci ba."

A wani sakon na daban kuma, ya soki shugaban kasa da mataimakinsa da kuma shugaban 'yan sanda.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Yobe Sunmonu Abdulmaliki, wanda shi ne ya bayar da umarnin kama Mista Japhet, ya ce rundunar na bukatar sanin "manufarsa ta yin hakan".

Wasu rahotanni sun ce rundunar sojin kasar ta fitar da wata sanarwa da ke jan hankalin "sojojin da su yi taka-tsantsan a duk huldar da za su yi da 'yan sanda" saboda rikicin da ya faru.

Shugaba Buhari ya kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin, bayan da ya gana da shugabannin rundunonin tsaron kasar.

Labarai masu alaka