Zakzaky zai koma Najeriya

Ibrahim Zakzaky Hakkin mallakar hoto Twitter/@SZakzakyOffice
Image caption An dade ana takaddama kan tafiyar Zakzaky Indiya

Shugaban kungiyar 'yan Shi'a ta IMN a Najeriya Ibrahim Zakzaky ya ce zai koma gida saboda rashin jituwar da ya samu da mahukuntan Indiya.

Tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin "bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa", sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan "mummunar halayyar da ya nuna".

A farkon watan nan ne wata kotu a Kaduna ta bai wa malamin da mai dakinsa Zeenat, izinin tafiya Indiya domin duba lafiyarsu bayan shafe shekara kusan hudu a hannun jami'an tsaron Najeriya bisa zargin tayar da zaune-tsaye da yunkurin kisa.

Tun bayan kama shi a watan Disambar 2015, ake samun taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayansa a kasar, inda aka yi hasarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama.

Mabiyansa da kuma masu kare hakkin dan'adam sun yi marhabin da hukuncin kotu, wanda ake ganin zai taimaka wurin kawo karshen kika-kakar da ake yi tsakanin kungiyarsa ta IMN da kuma jami'an tsaro.

Lamarin da ya kai ga haramta kungiyar da kuma ayyukanta.

'Dalilin barin Indiya'

Wannan bayani na dawowarsa gida Najeriya na kunshe ne a wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya.

Kuma za su kama hanyar dawowa nan da dan lokaci kadan.

Kawo yanzu babu bayani a hukumance daga mahukuntan Indiya ko kuma na Najeriya.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin kasar take rike da malamin addinin bayan wani rikici da mambobin kungiyarsa suka yi da sojoji a garin Zariya na jihar Kaduna.

Labarai masu alaka