Zakzaky na 'dab da isa' Najeriya

Ibrahim Zakzaky Hakkin mallakar hoto Twitter/@SZakzakyOffice
Image caption An dade ana takaddama kan tafiyar Zakzaky zuwa Indiya

Shugaban kungiyar 'yan Shi'a ta IMN a Najeriya Ibrahim Zakzaky ya ce zai koma gida saboda rashin jituwar da ya samu da mahukuntan Indiya.

Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya ne shugaban nasu zai sauka a filin jirgin sama na Abuja.

Tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin "bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa", sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan "mummunar halayyar da ya nuna".

A farkon watan nan ne wata kotu a Kaduna ta bai wa malamin da mai dakinsa Zeenat, izinin tafiya Indiya domin duba lafiyarsu bayan shafe shekara kusan hudu a hannun jami'an tsaron Najeriya bisa zargin tayar da zaune-tsaye da yunkurin kisa.

Tun bayan kama shi a watan Disambar 2015, ake samun taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayansa a kasar, inda aka yi hasarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama.

Me zai faru da shi idan ya sauka?

Ganin yadda aka samu kiki-kaka a Indiyar, da kuma yanke shawararsa ta komawa Najeriya, za a iya cewa zai koma hannun gwamnati ne kai tsaye kamar yadda yake kafin ya tafi Indiya.

Saboda izinin da aka bashi na tafiya asibiti ne kawai, ba wai beli ba ne.

Ibrahim Musa ya ce malamin zai sake neman komawa wata kasar ne tun da dai kotu ta riga ta ba shi damar zuwa a duba lafiyarsa.

"Babu wani rudani domin kotu ta riga ta bashi dama. Kuma Malam ya ce kasashen Turkiyya da Malesiya da Indunisiya dukka sun ce za su iya yi masa wannan aiki," a cewar Ibrahim Musa.

Sai dai wasu na ganin batun sake fitarsa ba lallai ne ya zo da sauki kamar yadda magoya bayansa ke hasashe ba, ganin irin takaddamar da batun zuwansa Indiya ya haifar tun farko.

Ana hasashen cewa idan har zai sake komawa kasar waje, to sai kotu ta sake bayar da wani sabon umarni, domin wannan umarnin na tafiya Indiya ne kawai kuma ya je ya dawo.

'Dalilin barin Indiya'

Kusan dai za a iya cewa a yanzu murna ta koma ciki ga mabiyan Zakzaky wadanda suka yi marhabin da hukuncin kotun, wanda ake ganin zai taimaka wurin kawo karshen kika-kakar da ake yi tsakanin kungiyarsa ta IMN da kuma jami'an tsaro.

Lamarin da ya kai ga haramta kungiyar da kuma ayyukanta da wata kotun tarayya a Abuja ta yi.

Wannan bayani na dawowarsa gida Najeriya na kunshe ne a wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya.

Kuma za su kama hanyar dawowa nan da dan lokaci kadan.

Kawo yanzu babu bayani a hukumance daga mahukuntan Indiya ko kuma na Najeriya.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin kasar take rike da malamin addinin bayan wani rikici da mambobin kungiyarsa suka yi da sojoji a garin Zariya na jihar Kaduna.