Rashida da Ilhan: Musulman da suka 'tsone wa Trump da Isra'ila ido'

Congresswomen Ilhan Omar (left) and Rashida Tlaib Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yar majalisar wakilan Amurka Ilhan Omar (daga hagu) da kuma Rashida Tlaib

Rashida Tlaib da Ilhan Omar sun kafa tarihi a watan Nuwamban 2018 lokacin da suka zamo Musulmai mata na farko da suka lashe kujerun majalisar wakilai a tarihin Amurka.

Duka matan dai mambobi ne na jam'iyyar Democrat kuma sun dace da irin siyasar kawo sauyi da jam'iyyar ke cewa tana yi.

Sun nuna goyon baya ga dokokin 'yancin dan adam, ciki har da na zubar da ciki da kuma goyon bayan masu zuwa ci-rani.

Sai dai akwai wani abu daya da ya sa suka raba-gari da sauran 'ya'yan jam'iyyar ta Democrat da ma na Republican: Isra'ila.

Kauracewa Isra'ila

Duka matan biyu na matukar sukar yadda Isra'ila take muzguna wa Falasdinawa, kuma su kadai ne 'yan majalisar da suka fito karara suka nuna goyon baya ga kungiyar Falasdinawan da ke jagorantar kaurace wa Isra'ila.

Wannan ya kuma sa Tlaib da Omar sun zamo 'yan majalisun Amurka na farko da aka hana shiga Isra'ila.

Hakan ya sha banban da takwarorinsu 72 da suka shafe wata guda suna wata ziyara a Isra'ila wacce masu neman kamun-kafa suka shirya kuma suka dauki nauyi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muftia Tlaib, wacce ke zaune a yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ita ce kakar 'yar majalisa Rashida Tlaib

Ilhan Omar da Rashida Tlaib suna shirin tashi zuwa Isra'ila ne domin shiga yankin Falasdinawa da ke karkashin mamayar Isra'ila: Gabashin birnin Kudus da Yammacin Kogin Jordan.

Ga 'yar majalisa Rashida Tlaib kuwa, tafiyar ta kunshi ziyarar danginta.

'Yar majalisar mai shekara 42, lauya ce daga Michigan amma 'yar asalin yankin Falasdinu, kuma har yanzu kakarta da sauran 'yan uwanta na zaune a yankin na Falasdinawa.

Bayan matakin na Isra'ila, Rashida Tlaib ta wallafa wani hoton kakarta a shafin Twitter, inda ta ce: "Matakin Isra'ila na hana jikarta, 'yar majalisar wakilan Amurka, shiga kasar alama ce da ke nuna cewa halin da Falasdinawa ke ciki na tayar da hankali ne."

Fafutukar 'yancin bakar fata

Ta kuma misalta hakan da yadda aka taba hana mai fafutukar wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, wato fitaccen dan siyasa na Amurka Jesse Jackson.

Rashida Tlaib ta ce Isra'ila kasa ce ta "'yan wariyar launin fata, abin da ita ma aka zarge ta da nuna "kin jinin Yahudawa".

Hakkin mallakar hoto GPO via Getty Images
Image caption Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump abokai ne sosai

Tana samun goyon baya a wannan fafutukar tata daga 'yar majalisa Ihan Omar daga Minnesota, 'yar shekara 38, wacce ke sanya dan kwali, 'yar asalin Somaliya, wacce ta iso Amurka a 1995 a matsayin 'yar gudun hijira.

Ta yi Allah-wadai da matakin hana su shiga Isra'ila, tana mai cewa abin kunya ne ga kasar da ke ikirarin cewa "ita kadai ce mai bin tafarkin demokuradiyya a yankin Gabas ta Tsakiya".

Zargin kin jinin Yahudawa

An zargi Ilhan da nuna kin jinin Yahudawa bayan wasu kalamai da ta yi a baya, amma daga bisani ta nemi "afuwa" tana mai gode wa abokan aikinta kan yadda suka ja hankalinta kan irin munin kisan kare-dangin da aka yi wa Yahudawa.

Sannan ta ce ta yi niyyar sukar kungiyoyin Yahudawa ne da ke kamun kafa a fagen siyasar Amurka, ba wai Yahudawa gaba daya ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Falasdinawa sun ce kungiyar da ke neman a kaurace wa Isra'ila halattacciya ce kuma ba ta dauke da makamai - amma Isra'ila na musanta hakan

Mutumin da ya yi fice wurin sukar su shi ne Donald Trump, wanda shi ma ya nemi Isra'ila da ta hana su shiga kasar.

Trump ya bayyana 'yan majalisar biyu da cewa "abin kunya" ne ga Amurka, sannan ya ce ba su izinin shiga kasar zai nuna gazawar Isra'ila.

"Sun tsani Isra'ila da dukkan Yahudawa, kuma babu wani abu da za a ce ko a yi da zai sauya zukatansu," kamar yadda ya wallafa a Twitter.

Dokar hana kauracewa Isra'ila

Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce an yi amfani da dokar hana kaurace wa Isra'ila wurin hana 'yan majalisar shiga kasar.

A karkashin dokar, wadda gwamnatinsa ta kafa a 2017, duk wani dan kasar waje da ya yi kiran a kaurace wa Isra'ila ta kowacce fuska - ba za a ba shi izinin shiga kasar ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption "Yan majalisar biyu sun musanta zargin cewa sun tsani Yahudawa

Isra'ila tana zargin kungiyar ta 'yan a kaurace mata da cewa tana barazana ga dorewar kasar, matsayar da 'yan siyasar Amurka da dama ciki har da 'yan majalisar kasar na duka jam'iyyun biyu suka amince da su.

Sai dai duka bangarorin biyu sun yi watsi da batun cewa kiran a kaurace wa Isra'ila tamkar kin jinin Yahudawa ne.

Labarai masu alaka