Barca ta fara La Liga da rashin sa'a 1-0 da Athletic Bilbao

Lokacin da Aritz Aduriz ya sheka wa Barcelona kwallo a raga Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau takwas Athletic Bilbao na cin kofin La Liga, amma yanzu shekara 35 rabonta da daukar kofin

Zakarun La Liga, Barcelona sun sha kashi a wasan bude gasar ta Sifaniya bayan da Aritz Aduriz ya yi kwance-kwance ya sheka musu bal din da ta ba wa Athletic Bilbao nasara.

'Yan wasan Barca ba su yi wani kwazo ba, wanda hakan ya sa Aduriz mai shekara 38, wanda ya shigo daga baya, ya sa su dandana kudarsu da cin da ya yi musu a minti na 89.

Luis Suarez da Rafinha kowannensu ya kai hari ta doki karfen saman raga, amma duk da haka bakin ba su burge ba a wasan duk da cewa sun sa sabon dan wasansu Antoine Griezmann da suka sayo daga Athletico Madrid a kan fan miliyan 107.

A karshe ma dai an fitar da Suarez saboda raunin da ya ji, tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Daman kuma Lionel Messi bai buga ba saboda jinyar raunin da ya ji a guiwa, yayin da shi kuma Philippe Coutinho, bai taka leda ba, saboda wasu rahotanni na cewa yana dab da tafiya Bayern Munich aro.

Kungiyar ta Ernesto Valverde wadda ke harin daukar kofin La Liga na uku, duk da ta sa sabon dan wasanta na tsakiya, Frenkie de Jong, wanda ta saya fan miliyan 65 daga Ajax, ta kasa tabuka komai a wasan, in banda hari biyu kwarara da ta kai.

Tsohon dan wasan tawagar Sifaniya wanda ya daga ragar Barcan, Aduriz, tuni ya sanar zai yi ritaya a karshen wannan kakar, bayan ya shafe shekara 20 yana taka leda.

Bal din da ya ci ta ba wa Athletic Bilbao, nasararta ta farko a gasar ta Sifaniya a kan Barcelona tun 2013, kuma ta kasance ta daya a tebur da maki uku a wasa daya, ita kuwa Barca ta kasance ta karshe a cikin kungiyoyin gasar 20.

Labarai masu alaka