Amurka ta ba da umarnin kwace jirgin man kasar Iran

Grace 1 supertanker sitting in the Strait of Gibraltar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Grace 1, yana daukar gangar danyen mai miliyan fiye da biyu

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta aike da sammacin kwace jirgin dakon mai na Iran da ke tsare, kwana daya bayan da wani alkali a Gibraltar ya ce a saki jirgin.

Jirgin mai suna The Grace 1 supertanker, wanda yake daukar gangar danyen mai fiye da miliyan biyu dai, an tsare shi ne a ranar 4 ga Yuli bisa zargin yin fasa-kaurin man zuwa kasar Syria.

Kokarin Amurkar na ci gaba da tsare jirgin ya ci tura bayan da wani alkali a Gibraltar ya yi watsi da hakan ranar Alhamis.

A baya dai Iran ta bayyana tsare jirgin Grace 1 da "haramtacce".

Mako biyu bayan da Amurkar ta kama Grace 1, ita ma Iran ta kwace wani jirgin ruwan Burtaniya mai suna Stena Impero a gabar ruwan Strait of Hormuz, ranar 19 ga Yuli.

Duk da cewa Iran din ta yi ikrarin cewa jirgin ya 'karya dokokin kasa da kasa', an yi amanna kwace jirgin na Burtaniya ramuwar gayya ce.

Me Amurka ta ce?

Wata babbar kotu a Washington ta aike wa da Majalisar Dinkin Duniya da duk wani mai karfin daukar hakunci sammacin kwace jirgin na Grace 1 mallakar Iran.

Takardar sammacin ta nemi da a kwace jirgin da man da yake dauke da shi. Ta kuma bayar da umarnin kwace $995,000 mallakar wani kamfanin kasar Iran, da ke ajiye a wani bankin kasar Amurka da ba a ambaci sunansa ba

Ma'ikatar Shari'ar ta ce jirgin da kamfanin duka suna da hannu a karya dokokin kasa da kasa da suka jibanci almundahana da safarar kudade da kuma ta'addanci.

Amurka dai na daukar sojojin kasar Iran na juyin-juya-hali a matsayin kungiyar 'yan ta'adda

Labarai masu alaka