Jirgin tankar mai na Iran ya baro Gibraltar

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hotunan cikin jirgin ruwan na Grace 1

Kasar Gibraltar ta sako wani jirgin ruwan Iran mai jigilar mai wanda ta kama tun watan Yuli.

Ta kama jirgin ne saboda ana tuhumar Iran da yi wa Syria jigilar mai wanda takunkmin karya tattalin arziki ya haramta haka.

Bincike ya nuna cewa tankar man ta nusa gabas kan hanyarta ta shia tekun Bahar Rum, amma babu wanda ya san inda ta nufa.

Kasar Gibraltar ta ki amincewa da wata bukatar da Amurka ta mika ma ta cewa ta ci gaba da tsare jirgin ruwan, wanda ya sauya sunansa daga Grace 1 zuwa Adrian Darya-1.

Amurkar ta yi wannan kokarin ne ranar Jumma'a, kwana daya bayan Gibraltar ta sallami jirgin.

Gibraltar ta kuma ce ba za ta iya sake tsare jirgin ba saboda takunkumin da Amurka ta sanya wa Syria ba su da tasiri a Tarayyar Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sauya wa jirgin ruwan suna zuwa Adrian Darya-1

Iran ta sanar da cewa za ta aika da wasu jiragenta na yaki domin raka tankar ta Adrian Darya-1.

Labarai masu alaka