Kotu ta yanke wa Ayuk Tabe hukuncin daurin rai-da-rai

Sisiku Julius Ayuk Tabe Hakkin mallakar hoto Sisiku Julius Ayuk Tabe/Twitter
Image caption Sisiku Julius Ayuk Tabe ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Ambazonia na farko

Kotun soji ta kasar Kamaru wadda Misse Njone ke jagoranta ta yanke wa madugun 'yan awaren Ambazonia, Sisiku Julius Ayuk Tabe tare da wasu mutum tara hukuncin daurin rai-da-rai.

Kotun ta kuma umarci madugun 'yan tawayen, Sisiku Ayuk Tabe da sauran mutum tara din da su biya ta tsabar kudi har sefa biliyan 250 da kuma karin sefa biliyan kusan 13 na kudaden da kotun ta kashe a kansu.

Sauran mutum taran su ne kamar haka;

  • Nfor Ngala Nfor
  • Tasang Wilfred Fombang
  • Henry Kimeng Cornelius
  • Njikimbi Kwanga
  • Fidelis Che
  • Che Augustin Awasum
  • Egbe Orock
  • Eyemba Elias Ebae
  • Shufain Blaise Sevidzem Beriynuy

Jagororin na Ambazonia dai sun yi batan dabo a wani otal a Najeriya, bayan da gwamnatin Kamarun ta kama su ta mayar da su gida domin gurfanawa a gaban kuliya

Kotun dai ta tuhumi mutanen 10 ne da laifukan tawaye da ta'addanci da rashin mallakar katin dan kasa da dai sauran laifuka, Sai dai a wani lokaci sun taba shaida wa kotun cewa su ba 'yan jamhuriyar Kamaru ba ne.

Image caption Sisiku Julius Ayuk Tabe da lauyoyinsa

Zaman kotun ya fara ne da misalin karfe 1:00 na ranar Litinin zuwa sanyin safiyar Talata lokacin da kotun ta yanke hukuncin.

Lauyoyin mutanen 10 dai za su hadu domin tattauna yiwuwar daukaka kara

Sisiku Julius Ayuk tabe dai ya jagoranci mutanen da suka ayyana kasar Ambazonia, inda kuma ya zamo shugaban kasar na rikon kwarya na farko.

Rikicin yankin renon Ingila a Kamaru yi sanadiyyar mutuwar mutum 2000 sannan ya raba mutum kimanin 500,000 da gidajensu, inda a yanzu haka akwai 'yan Kamaru masu gudun hijra a Najeriya su 33,000.

Labarai masu alaka