Yadda jarirai ke mutuwa a kauyen Chibiri, Abuja
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda jarirai ke mutuwa a wani kauyen Abuja

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Ana yawan samun mace-macen jarirai a wani kauyen da ke baban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja.

Hakan na faruwa ne saboda karancin asibitoci da likitoci, kamar yadda mazauna kauyen Chibiri suka shaida wa BBC kwanakin baya.

Mazauna kauyen suna da cibiyar lafiya guda daya tal ne, kuma babu gadon kwatar da marasa lafiya a cikin cibiyar.

Saboda haka idan aka samu mai nakuda da daddare to ya zama wajibi sai sun je babbar asibiti garin Kuje, wanda yake da nesa sosai daga kauyen .

Matan sun ce ba dukansu ne ke da kudin zuwa asibitin ba saboda haka "a lokuta da dama suke zabar su haihu a gida."

Wata da muka zanta da ita mai suna, Asabe Abdullahi, wacce tana daya daga cikin matan da suka rasa 'ya'yansu wajen haihuwa.

A cewar asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, kashi 10 cikin 100 na jariran da suka mutu a duniya a Najeriya suke.

Wannan na nufin jarirai 100 ne ke mutuwa a kowace haihuwa 1000.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka