Me ya sa harin Boko Haram ke karuwa a Niger da Najeriya?

An kai makamancin wannan hari a Borno kwana biyu da suka gabata Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mahukunta a kasar Nijar sun ce wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum 12 a garin Gueskerou na jihar Diffa da ke da kan iyaka da Najeriya.

Maharan sun kai hari garin Lamana a yankin Gueskerou ranar Juma'a, inda suka shiga garin a kan babura, kamar yadda mazauna garin suka shaida wa BBC.

Mazauna garin suka ce sun yi ta harbi cikin iska kuma sun halaka mutanen ne da wukake.

Maharan sun fice daga garin salin alin ba tare da wani dar ba domin kuwa babu jami'an tsaro a yankin.

Magajin Garin Gueskerou Hussaini Boucary ya shaida wa BBC cewa an binne wadanda suka rasun da safiyar Asabar.

An kai harin ne kwana biyu kacal bayan makamancinsa da aka kai a garuruwan Konduga da Gubio da Magumeri na jihar Borno.

Rahotonni sun ce mayakan Boko Haram ne wadanda ke biyayya ga kungiyar IS wato ISWAP suka kai harin.

An kashe sojan sa-kai daya kuma aka raunata daya da kuma farar hula da dama, sannan kuma abin ya shafi gidaje da wasu gine-ginen gwamnati.

Labarai masu alaka