Mun kai wa kasar Iran hari a Syria - Benjamin Netanyahu

Netanyahu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Netanyahu ya ce zai kashe makashinsa tun kafin ya kashe shi

Isra'ila ta ce ta kai wa wani wurin sojin kasar Iran a kasar Syria hari da manufar dakile yunkurin da Iran din ke yi na kai musu hari da jirage maras matuka.

Ba kasafai ba dai rundunar sojin Isra'ila ke bayyana ayyukansu a kasar Syria, to amma ta yi ikrarin kai harin sama ranar Asabar wanda ta ce ta kai kan 'jiragen Iran maras matuka masu kisa'.

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jinjina wa kokarin sojojin nasa na kai hari.

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Netanyahu ya ce "Ina jaddada cewa Iran ba ta da garkuwa a kowane wuri. Sojojinmu na ko'ina domin yakar zaluncin Iran. Kashe makashinka kafin ya kashe ka."

An dai yi amannar cewa Isra'ila ta gudanar da daruruwan hare-haren sama a Syria, tun bayan barkewar yakin basasa a kasar a 2011, da manufar hana kasar Iran samun wurin zama a Syria.

Mai magana da yawun sojin kasar ta Isra'ila, ya ce sun kai harin ne a kudu maso gabashin birnin Damascus na Syria.

Wasu majiyoyin sojojin kasar Syria da kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito na cewa sojoji sun dakile wasu jiragen yakin sama a tsibirin Golan a yunkurinsu na dosar birnin Damascus.

Wasu rahotanni sun ce jirage maras matuka mallakar Isra'ila sun sauka a wani sansanin 'yan kungiyar Hezbollah da Iran ke mara wa baya, a Beirut babban birnin kasar Lebanon.

Sai dai jagororin kungiyar Hezbollah sun ce wani jirgi maras matuki ya fado kan soron cibiyar watsa labaransu, inda jirgi na biyu shi kuma ya fashe a sama ya kuma fado kusa da ginin nasu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hezbollah ta wallafa hotunan tarkacen jirgin maras matuki da ta ce na kasar Isra'ila ne

Mazauna yankin a Beirut sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa sun ji karar fashewar wani abu da ya girgiza yankin, bayan jin kugin wani abu mai kama da jirgi. Sai dai Sojojij Isra'ila sun ki yadda su ce uffan kan wannan rahoto.

Firaiministan kasar Lebanon, Saad Hariri ya bayyana harin da Israila ta kai musu da na 'rashin mutunta kasa mai cin gashin kanta".

Rahotanni sun rawaito cewa Isra'ila ce ta kai wani hari ta sama a kan ma'ajiyar makaman kasar Iraqi a watan da ya gabata.

Jaridar The New York Times ta Amurka ta ambato wasu jami'an kasar Amurka na cewa Isra'ila ce ta kitsa harin saman da aka kai wa ma'ajiyar makaman na Iraqi a ranar 19 ga watan Yuli, bisa zargin cewa Iran na amfani da ma'ajiyar wajen safarar makamai zuwa cikin Syria.

Sojojin Isra'ila dai ba su ce uffan ba kan rahoton na The New York Times.

Labarai masu alaka