Da gaske ne gwamnatin Rivers ta rushe masallaci?

Vacant land
Image caption Mutanen da suke zaune a yankin da abin ya faru sun shaida wa BBC cewa an yi rusau din ne makon da ya gabata

Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Nyesom Wike ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta rushe wani masallaci a jihar.

Gwamna Nyeson Wike ya shaida wa 'yan jaridu cewa gwamnatin ta hana masu son gina masallacin yin gini, inda mutanen suka je kotu amma kuma gwamnati ta samu nasara a kansu.

A ranar Juma'a ne dai wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna taron masallata na sallar Juma'a a wani wurin da aka rushe da aka ce wani masallaci ne da gwamnatin jihar Rivers ta rushe da ke yankin Trans Amadi na birnin Port Harcourt.

Wannan batu dai ya janyo ka ce-na ce da tayar da jijiyoyin wuya a kafafen sada zumunta musamman tsakanin al'ummar kudu da arewa ko kuma tsakanin musulmi da kiristoci.

Gwamna Wike ya ce "Abun takaici ne a ce mutanen suna tunanin cewa sun gina masallaci amma gwamnati ta rushe musu".

Babban limamin masallacin na Trans Amadi, Alhaji Harun Mohammad, ya shaida wa sashen BBC na Broka cewa a 2010 ma gwamnati ta rushe masallacin ba tare da ba su wa'adi ba.

Ya kara da cewa sun kai gwamnatin gaban kuliya inda kotun ta damka musu filin kuma daga nan ne suka fara gina masallacin, kwatsam sai ga shi gwamnati ta sake rushe musu.

Mazauna yankin Rainbow na birnin Port Harcourt sun shaida wa BBC cewa a makon da ya gabata ne dai aka gudanar da rusau din.

Labarai masu alaka