Jama'a na tserewa daga yankin renon Ingila na Kamaru

Ayuk Tabe

Dubban mazauna yankunan renon Ingila na jamhuriyar Kamaru sun tsere daga gidajensu tun kafin fara aiwatar da dokar hana zurga-zurgar mako uku da 'yan tawayen Ambazonia ta sanar.

Rahotanni na cewa an samu rudani a tashoshin motoci sakamakon cinkoson dan adam, lokacin da jama'ar ke ta kokawar hawa motocin da za su bar garuruwan nasu saboda tsoron ka da dokar ta fara aiki suna nan.

A makon da ya gabata ne dai mayakan na Ambazonia suka ayyana lokacin zanga-zangar nuna rashin amince wa da hukuncin daurin rai-da-rai da wata kotun sojin kasar ta yanke wa jagororinsu guda 10, da suka hada da Sisiku Ayuk Tabe.

Sisiku Julius Ayuk tabe dai ya jagoranci mutanen da suka ayyana kasar Ambazonia, inda kuma ya yi ikrarin zamowa shugaban kasar na rikon kwarya na farko.

Yankunan renon Ingila na zargin jamhuriyar Kamaru da mayar da su saniyar ware da kuma fifita masu magana da Faransanci a kansu.

Rikicin yankunan renon Ingila dai ya fara ne a 2016, lokacin da lauyoyi da malaman makaranta suka tsunduma yajin aiki kan kokarin gwamnati na kakaba musu harshen Faransanci a makarantu da kotu da ke Arewa Maso Yammaci da Kudu Maso Yammacin kasar.

Wasu tuni suka dauki makamai a 2017, inda daruruwan mutane suka mutu sannan fiye da mutum 500,000 sun bar mahallansu.

Image caption Daruruwan mutane sun bar mahallansu a 2015 a yankunan na Kamaru

Hukuncin kotun Soji

A makon da ya gaba ne dai wata kotun soji a Kamaru wadda Misse Njone ke jagoranta ta yanke wa madugun 'yan awaren Ambazonia, Sisiku Julius Ayuk Tabe tare da wasu mutum tara hukuncin daurin rai-da-rai.

Kotun ta kuma umarci madugun 'yan tawayen, Sisiku Ayuk Tabe da sauran mutum tara din da su biya ta tsabar kudi har sefa biliyan 250 da kuma karin sefa biliyan kusan 13 na kudaden da kotun ta kashe a kansu.

Sauran mutum taran su ne kamar haka;

  • Nfor Ngala Nfor
  • Tasang Wilfred Fombang
  • Henry Kimeng Cornelius
  • Njikimbi Kwanga
  • Fidelis Che
  • Che Augustin Awasum
  • Egbe Orock
  • Eyemba Elias Ebae
  • Shufain Blaise Sevidzem Beriynuy

Jagororin na Ambazonia dai sun yi batan dabo a wani otal a Najeriya, bayan da gwamnatin Kamarun ta kama su ta mayar da su gida domin gurfanawa a gaban kuliya

Kotun dai ta tuhumi mutanen 10 ne da laifukan tawaye da ta'addanci da rashin mallakar katin dan kasa da dai sauran laifuka, Sai dai a wani lokaci sun taba shaida wa kotun cewa su ba 'yan jamhuriyar Kamaru ba ne.

Zaman kotun ya fara ne da misalin karfe 1:00 na ranar Litinin zuwa sanyin safiyar Talata lokacin da kotun ta yanke hukuncin.

Lauyoyin mutanen 10 dai za su hadu domin tattauna yiwuwar daukaka kara

Labarai masu alaka