Me ya sa Donald Trump ke neman sulhu da kasar Iran?

Iranian President Hassan Rouhani speaks in Tehran on 27 August 2019 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Trump da Hassan Rouhani dai za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a watan Satumbar nan

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya bukaci Amurka da ta fara cire wa kasar takunkuman da ta kakaba mata a matsayin matakan farko na neman tattauna wa da Iran.

"Idan har ba a dauki matakin cire takunkumin ba, ba za a iya bude wannan dan mukullin ba," in ji Rouhani.

Rouhani ya fadi hakan ne kwana daya bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce kofarsa a bude take domin tattauna wa da kasar ta Iran idan har akwai bukatar hakan.

Rikici tsakanin Amurka da Iran dai ya ta'azzara tun bayan da Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar takaita shirin nukiliyar Iran a bara, sannan kuma ya sake kakaba wa Iran din jerin takunkumi.

Shi dai Donald Trump na son a sake yarjejeniyar da za ta taka wa Iran burki kwata-kwata ka da ta ci gaba da shirin samar da nukiliya, batun da Iran ta ki amincewa da ita.

Sauran manyan kasashe da suke cikin yarjejeniyar ta 2015 wato Burtaniya da Faransa da Jamus da China da kuma Rasha sun yi kokarin ci gaba da mutunta ta to amma jerin takunkuman da Amurkar ta kakaba wa Iran ya janyo sakwarkwacewar tattalin arzikin kasar.

Kasashen duniya sun daina sayen man kasar Iran sannan darajar kudinta ta karye baya ga tashin gwauron zabbi da farashin kayayyaki ya yi.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa shi da Donald Trump na Amurka sun yarda da cewa ya kamata a tattauna da Iran. Amma ba su amince da ci gaba da ayyukan samar da makaman nukiliya ba.

Me Donald Trump ya ce?

A ranar Litinin ne dai yayin wani jawabi ga manema labarai na hadin gwiwa a lokacin taron kasashe bakwai masu tattalin arzikin duniya a Biarritz, shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya fada wa Hassan Rouhani na Iran ta waya cewa "Ya gamsu cewa za a iya cimma matsaya" idan har zai yarda ya hadu da mista Trump.

"Abin da nake fata a makonni masu zuwa...za mu iya ganin yadda za mu gana."

Mista Trump ya ce ganawar da za su yi ta gaskiya ce, inda ya kara da cewa Iran za ta samu rancen kudade daga kasashen duniya domin ta tayar da komadar tattalin arzikin da ta yi fama da shi.

"Ina ji a jikina cewa Rouhani zai so ya yi wannan ganawar domin fitar da kasarsa daga kangin da take ciki. Iran na fama da wahala."

Mista Trump da Hassan Rouhani dai za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a watan Satumbar nan.

Taron ne zai zama wani wuri da shugaban Amurka da na Iran za su hadu a karon farko tun shekarar 1979-81 lokacin da kasashen biyu suka samu rashin fahimta bayan juyin juya-halin kasar Iran.

Mene ne martanin Hassan Rouhani?

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce takunkuman Amurka 'haramtattu ne kuma babu adalci a cikinsu'

A wani jawabin da ya yi ta gidan talbijin yayin wani taro a birnin Tehran ranar Talata, shugaba Hassan Rouhani ya ce a koyaushe kofarsa a bude take domin tattaunawa to amma fa "sai Amurkar ta fara cire jerin haramtattun takunkuman da ta kakaba wa kasar tasa."

Ya kara da cewa "Idan Amurka ba ta cire takunkumin ba kuma Shugaba Trump bai yi watsi da matakin da kasar take dauke ba, ba bu wata tattaunawar arziki da za mu cimma. Cimma wannan yarjejeniyar kacokan na hannun Amurka ne."

Hassan Rouhani ya kuma ce "idan abin da ke bai wa Mista Trump tsoro shi ne batun shirin nukiliyar Iran, to ya sha kuruminsa".

"Ba mu da burin mallakar makaman kare dangi ko makaman nukiliya, ba kuma mun ki mallaka ba ne saboda Amurka ba ta so ko kuma saboda gargadin da suke yi wa duniya, sai dai kawai saboda irin abin da muka yi imani da shi da kuma fatawar da shugaban addininmu."

Shugaban addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya fitar da wata Fatawa a 2013 da ta yi watsi da mallakar makaman nukiliya.

To sai dai kasashen duniya ba su amince da cewa Iran din ba ta bukatar mallakar makaman nukiliya

Labarai masu alaka