Bikin Ranar Hausa a Sudan
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ranar Hausa: An baje kolin al'adun Hausa a Sudan

Al'ummar Hausawan Sudan sun bi sahun miliyoyin Hausawan duniya inda suka gabatar da bikin Ranar Hausa a babban birnin kasar, Khartoum.

A taron dai an gabatar da wasu lambobin yabo ga wasu mutane saboda irin gudunmuwar da suka ba Hausa a fadin duniya.

Daga bisani kuma an nishadantu da wakokin Hausawan Sudan an kuma baje kolin al'adun Malam Bahaushe.

Labarai masu alaka