An kai wa Iran hari ta intanet

Iran

Masu kutse a yanar gizo da ke wa gwamnatin Amurka aiki sun lallata kwamputoci mallakar dakarun tsaron kasar Iran wadanda suke amfani da su domin shirya hare-hare ga jiragen dakon mai.

Jaridar New York Times ta ce wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa Amurkar ta taba yin irin wannan kutsen a watan Yuni.

Wannan ya faru ne a ranar da Mista Trump ya dakatar da ramuwar gayyar da yayi niyyar kai wa Iran, bayan sun harbo wani jirgi mara matuki mallakar Amurkar.

Rahotanni sun bayyana cewa Iran na nan na kokarin kara tattara bayanai da kuma kara inganta kwamputocin da kutsen Amurkar ya lalata.

A wani bangare kuma sakataren tsaron Amurka Mark Esper ya bukaci Iran da ta tattauna da Amurka domin rage fargabar da ke yankin Gulf

Labarai masu alaka