'Mahaifina ya tsine min don na ki bin zabinsa a aure'

  • Fauziyya Kabir Tukur
  • BBC Hausa, Abuja
Auren dole na daya daga cikin manyan abubuwan da ke janyo karuwar mutuwar aure

Hawaye na gangarowa daga idanunta, cikin murya mai sarkewa Ladidi (ba sunanta na asali ba)ta bayyana min labarinta.

"Ana gobe daurin aurena, na je na sami babanmu na ce ya ba ni kudi zan je lalle sai ya ce ai ban da ni za a daura wa aure. Daga baya da adddare sai ya kira ni ya ce in shirya gobe zamu je a yi min test (gwaji) domin za a daura min aure da wani.

"Ni kuma bana son sa, sai Ummata ta goyi bayana muka je wajen Hisba aka warware auren" in ji Ladidi.

Ladidi, mai shekara 16 ta kasance kamar ko wace mace a yankunan karkara a arewacin Najeriya, wato tana fara tasawa aka fara yi mata maganar aure.

Masoya sun yi mata ca, kuma ta fitar da mutum daya da take so ta aura- iyaye suka shiga maganar har aka sa ranar aure.

Bayanan hoto,

Ana samun karuwar mata masu neman a bi masu hakkinsu a arewacin Najeriya

Amma kwana guda tal kafin a daura auren, sai mahaifin Ladidi, Malam Ali ya sauya shawara, ya ce ya fasa bayar da ita ga wanda ta fitar kuma ya yi mata sabon zabi- hukuncin da Ladidi ta yi fatali da shi kamar yadda ta shaida min.

Ladidi da mahaifiyarta sun garzaya ga Hukumar Hisba ta jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya don ta sa baki a lamarin.

Hukumar ta saurari korafin Ladidi kuma ta kira Malam Ali domin a yi maslaha a lamarin.

Daga karshe mutumin da aka aura wa Ladidi ya sake ta bisa umarnin hukumar Hisba.

Sai dai mahaifin Ladidi ya musanta kalaman 'yarsa.

Ya ce ana saura kwana 15 a daura auren Ladidi mahaifiyarta ta sauya magana, ta ce ba ta son Ladidi ta auri mijin da ta fitar.

Ya kuma ce ta yi haka ne domin tana so Ladidi ta auri wani dan uwanta.

Lokacin da ya kamata ya zamo na farin ciki ga Ladidi ganin an raba ta da wanda ba ta so, ya zama na kunci da fargaba.

Domin kuwa mahaifinta ya yi furucin da zai jefa ko wane da a kunci, wato ya tsine mata.

"Duk abin da nai mata daga cikinta zuwa yau ban yafe mata ba. Na ce ta je ta auri duk wanda take so. Kuma na sake daukar mataki na ce duk 'yan uwa na ba wanda zai je daurin auren," a cewarsa.

Hukumar Hisba

Hukumar Hisba wacce ke aiki da dokokin addinin musulunci, kan yi ruwa ta yi tsaki a irin wadannan lamurra na rashin jituwa tsakanin iyaye da 'ya'yansu dalilin aure.

A tsakanin wasu al'ummomi na arewacin Najeriya, ana kallon mutuwar aure a matsayin wani abin assha musamman idan mace ce ta nemi saki.

Sau da yawa, matan da aurensu ya mutu kan fuskanci tsangwama a tsakanin al'umma wani lokaci ma daga danginsu kamar yadda ya faru da Ladidi.

Bayanan hoto,

Malam Ibrahim Dahiru Garki kwamandan Hisba na jihar Jigawa

Malam Ibrahim dahiru Garki, kwamandan Hisba na jihar Jigawa ya ce suna ganin irin wadannan matsalolin da dama.

"A cikin shekaru hudu mun yi wa mata a kalla 9821 sulhu tsakaninsu da iyayensu da kuma tsakaninsu da mazajensu, amma wanda aka yi wa tsakaninsu da mazajensu sun fi yawa" a cewarsa.

Ya kuma ce kafin a kafa hukumar a jihar, matan da suka kashe arensu musamman dalilin auren dole kan fada halin ha'ula'i.

Ya ce "sai ka ga yarinya ta shiga karuwanci, ko ma ta kashe kanta. Amma a yanzu hukumar Hisba na shigowa ta tabbar an samu maslaha."

Malam Ibrahim ya bayyana cewa hukumar Hisba ba ta raba aure, illa dai ta yi sulhu. Sai dai wani lokaci ta kan mika lamarin ga kotun addinin musulunci domin yanke hukunci.

Tsangwama

Dakta Rafatu AbdulHamid, malama a jami'ar Abuja kuma mai bincike kan rayuwar aure a kasar Hausa ta ce karuwar mace-macen aure yanzu ya zama abin damuwa.

Ta ce a yanzu dan karamin al'amari da bai kai ya kawo ba kan ja miji ya saki matarsa ko ita matar ta bukaci a sake ta.

A wata makala da ta buga a mujallar Journal of Arts and Humanities, Dakta Rafatu ta ce mafi yawan abubuwan da suke jawowa auren ya mutu sun hada da rashin ciyarwa da duka.

"Za a ce ta fita, wani lokaci ma mijin zai kulle kofa ta koma gidan iyayenta babu mamaki ba su da karfi iyayen, ganinta iyayen su kuma wani karin damuwa ne.

"Wata daya wata biyu sai su fara gajiya da ita, sai ki ga ta shiga wani hali. Gidan miji an sake ta, gidan iyaye ba nutsuwa ba kwanciyar hankali." in ji Dakta Rafatu.

Bayanan hoto,

Barrister Huwaila Ibrahim

Barrister Huwaila Ibrahim lauya a jihar Kano ta bayyana cewa yawan matan aure da ke zuwa neman taimako a kotu na karuwa.

"Babu al'amarin da ya ta'azzara a wannan yankin namu kamar duka da rashin ciyarwa", a cewarta.

Sai dai ta ce abin takaici shi ne matan ba sa samun goyon bayan iyayensu.

"Iyayenmu na da kawaici, ko yarinya na da matsala a gidan miji sai a ce kije ki ta hakuri nima da kika gan ni hakuri nake ta yi tunda na yi aure," a cewarta.

"Su dai kawai kada a ce 'yarsu ta fito daga gidan miji" in ji Barrister Huwaila.

Malam Ali ya saki mahaifiyar Ladidi dalilin wannan takaddama.

"Ni dai ni ne uban yarinyar nan kuma na shirya za a yi bikin nan, na sai kayan daki na yi komai ta ce bata yarda, toh na ce tunda haka ne aure an fasa wannan an fasa wancan" in ji Malam Ali.

Irin wannan dai ba sabon abu ba ne, mutuwar auren 'ya'ya kan zama silar lalacewar auren iyayensu.

Ana iya cewa wannan tatagurza tsakanin wadannan mahaifa ba zai fitar da 'yarsu daga kangin da take ciki ba, illa ma dai ta sake tsunduma ta cikin rudani.

Ladidi ta shaida min cewa tana so ta sake aure nan gaba, ga wanda take so.

Sai dai kuma mahaifinta ya ce yana nan a kan bakansa, domin kuwa babu ruwansa da ita.

"Ba na so ta bata da mahaifinta, ba na so 'yata ta shiga wani hali shi ya sa nake so ta shirya da babanta" in ji mahaifiyar Ladidi.

Ta ce babu abin da bata yi ba don ganin ta shirya Ladidi da mahaifinta.

Mahaifiyar Ladidi ta ce "gaba daya magabantansa sun yi bakin kokarinsu ba yadda ba a yi ba hatta mahaifiyarsa ta sa baki amma ya ki amicewa ya yafe mata."

Ana iya cewa hisba ta tsaya wa Ladidi wajen raba ta da auren dole, kuma kwamanda Ibrahim Dahiru ya ce hukumarsa za ta yi sa baki a rigimar da ta barke a gidansu Amina.

Abin dubawa a nan shi ne, ko ayyukan hukumar hisba na tasiri mai dorewa a rayuwar mata a jihar Jigawa?

'Yan watanni da suka gabata ne hukumar ta tsaya har aka raba aure sama da 300 a jihar dalilin auren dole ko auren wuri, ciki har da auren Ladidi.

Sai dai abin dubawa a nan shi ne- ko mece ce makomar wadannan mata?

Da yawansu dai ba su da ilimi sannan ba su da sana'ar yi.

Ga tsangwama da wulakanci da za su iya fuskanta daga al'uma.

Duka wannan na iya jefa wadannan mata cikin halin ni 'ya su.