Hikayata ta sa na zama uwar marayu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Na cika burina na tallafa wa marayu dalilin gasar Hikayata'

Gwarzuwar Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Hikayata ta 2018 Safiyya Jibril Abubakar ta ce gasar ta kawo sauye-sauye da dama na alheri a rayuwarta.

Ta ce gasar ta sauya yadda mutane ke kallonta, kuma ita kanta tunaninta ya sauya dangane da rubutun Hausa.

Haka kuma ta ce ta samu damar cika burinta na tallafa wa marayu.

"Na yi amfani da kyautar da na samu na inganta rayuwar wasu marayu a arewacin Najeriya."

Sashen Hausa na BBC ya kirkiri gasar rubutu ta Hikayata ne domin bai wa mata zalla damar a dama da su a harkar rubutun adabin Hausa kuma ana gudanar da ita ne duk shekara.

Alkalan gasar kan zabi mutum uku wadanda labaransu suka zarce saura domin ba su kyautuka, wadanda kuma a cikinsu ne za a zabi gwarzuwa. A'isha Sabitu ce gwarzuwar gasar ta 2016 yayin da Maimuna Idris Sani Beli ce gwarzuwar gasar ta 2017.

Labarai masu alaka