Yadda ambaliyar ruwa take barna a Abuja
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda ambaliyar ruwa take barna a Abuja

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Ambaliyar ruwa ta ci gaba da barna a fadin Najeriya.

Wannan gadar a Apo ta karye ne sakamakon ruwan sama da ake ta yi ba kakkautawa a Abuja, babban birnin kasar.

Hakan ya sa dole motoci ke tsayawa sai ruwan ya dan lafa kafin su wuce.

Mazauna unguwar sun yi kira ga gwamnati da su agaza masu a gyara wannan hanyar.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, Injiya Mustapha Y Maihaja ya yi gargadin cewa jihohi 30 na fuskantar barazanar ambaliya.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka