Iyaye na son a haramta wa yara zuwa makaranta da waya

A school pupil in uniform using a smartphone at their desk Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana samun karuwar yara da ke kai wayoyi makaranta

Kashi 49 cikin dari na iyaye a Birtaniya na ganin cewa ya kamata makarantu su haramtawa yara zuwa makaranta da waya, a cewar wani bincike da shafin intanet na uSwitch ya yi.

Binciken, wanda ya kunshi sama da mutane 1000, ya nuna cewa matskaiciyar darajar wayoyin da ko wane yaro ke kai wa makaranta ya kai Fam 301.

A bara ne sakataren al'adu na wannan lokacin Matt Hancock ya ce makarantun da suka haramta wa yara kai waya sun birge shi.

Sai dai wasu na ganin hana yara kai waya makaranta zai toshe masu damar koyon sanin-ya-kamata.

Binciken, wanda Opinium ya gudanar a madadin uSwitch, ya bayyana cewa matskaiciyar darajar wayoyin da yara ke kai wa makaranta na karuwa.

An yi hasashen cewa a shekarar 2019, darajar duka wayoyin da ake kai wa makaranta a fadin Burtaniya zai kai Fam biliyan 2.3.

Haka kuma, kashi 43 cikin dari na yara na da sabuwar samfurin waya, wadda kuma iyayensu ba su da irinta, kuma gaba daya abin da manya ke kashewa kan kudin wayar da 'ya'yansu suka tara ya kai Fam biliyan 13.

"Yawan wayoyin da yara ke kai wa makaranta ya wuce misali." in ji Ernest Doku, wani masani kan harkar wayoyi a uSwitch.

Ba abin mamaki ba ne idan iyaye suka nuna damuwarsu kan cewa waya za ta dauke hankalin yara a makaranta, amma Mista Doku ya ce haramta wayoyin ba ita ce mafita ba.

Ya ce "Iyaye da yawa na son su san inda 'ya'yansu suke idan wani bala'i ya afku, ko kuma idan ba su dawo gida a lokacin da suka saba ba ta hanyar kiransu ko amfani da manhaja."

A shekarar 2018, shugaban Eton ya ce bai kamata makarantu da iyaye su ji tsoron kwace wayoyi daga hannun yara ba.

Ba kowa ne ya amince da wannan tsarin ba.

Wasu na ganin cewa lokaci ya zo da akwai waya a ko ina, don haka bai kamata a ware yara a hana su damar amfani da ita ba.

"Idan amfanin makaranta da ilimi shi ne don mu iya zaman duniya, koyon amfani da waya na da matukar muhimmanci kenan," in ji Pail Howard-Jones, wani farfesa a Jami'ar Bristol.

"Ya kamata yara su san ya-kamata. Idan aka kwace masu wayoyinsu attafari, lallai an toshe masu damar sanin ya-kamata," a cewarsa.

Labarai masu alaka