Aminu Masari: Gwamnan Katsina zai yi sulhu da masu kai hari

Aminu Bello Masari
Image caption Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya ce zai shiga daji domin sasantawa da masu kai wa jama'ar jiharsa hare-hare

Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta tattauna da mutanen da ake zargi da kai hare-hare da satar mutane domin kudin fansa don kawo karshen matsalar tsaro da take addabar jihar a kwana-kwanan nan.

Daraktan yada labaran gwamnan jihar, Audu Labaran, ya shaida wa BBC cewa a wannan karon gwamna Aminu Bello Masari zai shiga daji domin tattaunawa da maharan.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da aka yi a fadar gwamnatin ta Katsina.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan wasu mahara sun akfkawa garin Wurma a karamar hukumar Kurfi, inda aka sace mata da dama.

Wadanda suka halarci sun hada da gwamna da mataimakinsa da sakataren gwamnati da Sarkin Katsina da shugabannin hukumomin tsaro da shugabannin kungiyoyin Fulani da kuma wasu masu kai hare-haren da suka ce sun tuba.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/BUHARI SALLAU
Image caption A ba ya gwamnatin Aminu Bello Masari ta ce duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane da satar shanu za a yi masa hukuncin kisa

A cikin hirar, daraktan ya bayyana cewa a lokacin taron da aka yi na Katsina da gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya an amince cewa "kowacce jiha ya kamata ta kawo kudi ina jin miliyan 100, a hada kudin nan, wato a hada karfi da karfe a yaki wannan abin tun kafin ya zama wani abu daban" a cewarsa.

Ya ce "to a bayan hakan ne gwamnonin suka yi shawarar ba shi mukamin Ciyaman na din-din-din. Amma tun bayan taron babu wani wanda ya kara waiwayar abin da aka yi ban da shi gwamna Masarin".

Ku saurari cikakkyiyar hirar Editanmu na Abuja Yusuf Ibrahim Yakasai da daraktan watsa labaran gwamnan, Abdu Labaran kan wannan sabon mataki:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Batun tsaro a jihar Katsina

Hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don kudin fansa na ci gaba da karuwa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen matsalar da ta addabi yankin arewa maso yammacin kasar.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihohin.

Kananan hukumomin da matsalar ta tsafa a jihar Katsina sun hada da Jibia da Batsari da Danmusa da Safana da Kankara da Sabuwa da Faskari da kuma Dandume.

Labarai masu alaka