Dara ta ci gida, an yi wa mai kamfanin Twitter kutse

Jack Dorsey Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata kungiya mai suna Chuckling Squad ta dauki alhakin kutsen da aka yi wa shafin Twitter na Jack Dorsey na dan wani lokaci.

Shafin na Jack Dorsey dai na da mabiya fiye da miliyan hudu, kuma an yi amfani da shafin nasa wajen wallafa sakon muzantawa da nuna wariyar launin fata ga Yahudawa tare kuma da yin ba'a ga ikrarin kisan gilla da Yahudawan ke kokarin fahimtar da duniya gaskiyarsa wanda ake kira 'Holocaust'.

Sakon dai ya kwashe kimanin minti 15 a shafin Twitter, inda har mabiyansa da dama su ma suka yi ta kara wallafa sakon ta hanyar kambama shi.

Kamfanin Twitter ya ce ba bu abin da ya shafin na'urorinsu, illa dai kamfanin ya zargi wani kamfanin wayar salula da ba a ambaci sunansa ba.

"Lambar wayar Jack Dorsey da ke damfare da shafin nasa na Twitter ta samu matsala sakamakon 'yar matsalar tsaro da kamfanin wayar ya samu," In ji kamfanin na Twitter.

"Hakan ne ya bai wa wani damar kirkirar sako da aike wa da sakonnin Twitter ta sakon wayar hannu daga lambar. Amma yanzu an magance matsalar."

Yadda aka yi kutsen

Wata majiya a kamfanin na Twitter ta shaida wa BBC cewa masu kutsen sun yi amfani da wata dabara da ake kira "simswapping" ko kuma "simjacking" domin jujjuya akalar shafin Mr Dorsey.

Wannan dai wata dabara ce ta yadda ake amfani da lambar wayar mutum, a kan sabon layin waya musamman bayan masu kutse sun shammaci ko kuma sun bai wa ma'aikatan kamfanin waya toshiyar baki.

Ta hanyar rike linzamin lambar, masu kutsen sun samu nasarar wallafa sakonnin Twitter ta hanyar aike wa da sakon waya zuwa shafin Twitter na Mr Dorsey.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dorsey, mai shekara 38 ya kasance buloniya kuma yana shugabantar kamfanoni guda biyu

Labarai masu alaka