Aisha Buhari ta ja kunnen masu rike da mukamai

Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Instagram/AishaMBuhari
Image caption Aisha Buhari ta dade tana jan kunnen shugabanni game da al'amura daban-daban

Uwar Gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Aisha Buhari ta jinjina wa malamai masu bayar da shawara ga shugabannin al'umma tare da shawartar masu rike da mukamai da su yi aiki da abin da suke fada.

Ta yi wannan kira ne a shafinta na Instagram bayan ta wallafa wani bidiyo da ke nuna Dakta Abdallah Usman Gadon Kaya yana wa'azi ga shugabannin Najeriya.

A cikin bidiyon, Abdallah Gadon Kaya ya koka kan yadda shugabanni ke sace kudin kasa "a lokacin da ba ma iya zuwa jami'o'i da asibitoci".

Aisha Buhari ta wallafa bidiyon tare da taken: "Hattara ga masu rike da mukamai! Wallahi Allah ya dora mu kan mulki da kuma kokarin malamai da talakawa! Don Allah mu bi shawararsu mu yi wa al'umma adalci! Subhanallah!

Mutum sama da 150 ne suka mayar wa da Uwar Gidan Shugaban Kasar martani tare da bayyana mabambantan ra'ayoyi:

@isad08: Allah yasa sako ya isa ga megida

@am_modassir: Gsky ne Allah yabamu ikon fahim tar gsky da kuma yin aeki da ita Ameen

@fatihu_m_ahmad: Me yasa mutane basa taba barin su fahimci gaskia saboda adawa ko son rai.....? Ba cewa taci su adalai bane ko suna kan dai_dai, fadakarwa ce de wannan KYAUTA

@nagarta_fashion_design: Dan Allah a bawa me gida ya ji

"Ina kira ga shugabanni masu satar kudin bayin Allah, su gina gidaje da kudin mutane, su tafi kasashen waje da kudin mutane. Akwai dabbanci da rashin hankali," Abdallah Gadon Kaya ya koka a cikin bidiyon.

"Kowa idan garin Allah ya waye fita yake ya nemi abin da zai ci amma shi kuma wani ya kwanta a kan dukiyarmu yana abin da ya ga dama da ita."

Malamin har wa yau, ya koka kan yadda gwamnoni ke yin mursisi har sai al'umma sun roke su da su yi wa kasa aiki.

Ba wannan ne karon farko da Aisha Buhari take yin kira ga masu iko a Najeriya ba ta hanyar wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta.

A ranar 24 ga watan Mayu ta wallafa bidiyon wani dan majalisar kasar Afirka Ta Kudu a shafinta na Twitter, inda yake jan kunnen sabon shugaban kasar Cyril Ramaphosa da ya saurari shawarar al'umma ko kuma shi ma su tsige shi.

Ta rubuta "#listentoadvise #teamwork", abin da ke nufin "saurari shawarwari yin aiki tare".

A ranar Alhamis din da ta gabata ma ta wallafa wani sakon a Instagram tana mai neman mutane su tashi tsaye da addu'a domin ceto al'ummar jihar Katsina da Najeriya baki daya daga halin rashin tsaro da ake ciki.

'Mace mai jawo ce-ce-ku-ce'

Ana yi wa Hajiya Aisha Buhari kallon mace mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan al'amuran da suka shafi mulkin maigidanta.

Ta taba yin wata hira da BBC Hausa, inda ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijninta, Shugaba Muhammadu Buhari, suna hana ruwa gudu.

Akwai kuma lokacin da ta soki jam'iyya mai mulki ta APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Labarai masu alaka