Hotunan rikicin kin jinin baki a Afirka Ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sandan Afirka ta Kudu na sintiri a unguwar Alexandra ta birnin Johannesburg ran 3 ga watan satumbar 2019 bayan da rikicin kin jinin baki ya barke a birnin. Rikicin ya sake barkewa a dare na biyu a birnin na Johannesburg inda daruruwan mutane suka yi tattaki a tituna ranar 2 ga watan satumba a wani mataki da ba a saba ganin irinsa ba na nuna tsananin kin jinin baki.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani jami'in tsaro na farin kaya na sintiri a unguwar Alexander a birnin Johannesburg ranar 3 ga watan satumba, 2019.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaro na farin kaya a lokacin da rikicin ya barke. Rikici ya barke a dare na biyu a unguwar Alexander a birnin Johannesburg inda daruruwan mutane suka yi tattaki a tituna ranar 2 ga watan satumba a wani mataki da ba a saba ganin irinsa ba na nuna tsananin kin jinin baki.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaro na karawa da barayi a lokacin rikicin kin jinin baki ran 2 ga watan satumba 2019 a birnin Johannesburg a Afirka ta Kudu.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sace kaya tare da kona shaguna a wasu unguwannin Johannesburg, wanda mafi yawa shagunan baki ne.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magajin garin Lardin Gauteng David Makura yana magana da manema labarai a unguwar Alexander da ke Johannesburg.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani bako yana dauke kayansa daga wani shago da aka fasa a Johannesburg ranar 3 ga watan Satumbar, 2019

Labarai masu alaka