Boko Haram: Shin kungiyar ta ce za ta kai wa Afirka ta Kudu hari?

A Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a san adadin mutanen da suka rasa ransu ba sanadiyyar hare-haren da ake kai wa baki 'yan kasashen waje a wannan makon a Afirka ta Kudu

Tun bayan fara kai wa 'yan kasashen waje hare-hare a farkon makon nan a Afirka ta Kudu ake ci gaba da samun wasu labaran bogi wadanda ake yadawa a kafafen sada zumunta musamman a Najeriya.

Akwai wani rahoton da ya yi ikirarin cewa kungiyar Boko Haram ta ce za ta kai wa Afirka ta Kudu hari a matsayin martani game da yadda wasu 'yan kasar suke kai wa baki farmaki.

Sai dai binciken da muka yi dangane da wannan labarin ya gano cewa babu kamshin gaskiya game da wannan ikirari na barazanar kai harin.

Image caption Shafin ₦airaland Forum ya wallafa labarin ikirarin Boko Haram za ta kashe 'yan Afirka ta Kudu hari a ranar Talata

Iya bincikenmu babu wata sanarwa da ta fito daga kungiyar dangane da wannan labarin ta kafofin da suka saba fitar da sanarwa.

Hakazalika an rika yada irin wannan labarin da kuma wasu tsoffin faya-fayan bidiyo da ke ikirarin nuna yadda ake kai wa 'yan Najeriya hare-hare a Afirka ta Kudu.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Akwai alamomi da suke nuna cewa bidiyon ba daga kasar Afirka ta Kudu ya fito ba

Jama'a sun rika yada wani bidiyo a musamman a manhajar WhatsApp wanda yake ikirarin nuna yadda wasu mutane baki 'yan kasashen waje suke dirowa daga wani bene a Afirka ta Kudu.

Sai dai binciken da wani shafin da ke yaki da labaran boge wato Africa Check ya yi, ya gano cewa wani tsohon bidiyo ne, na wani bene da ke jihar Gujarat a kasar Indiya da ya kama da wuta kuma an fara wallafa shi ne tun a watan Mayun da ya wuce.

Bugu da kari, akwai wasu alamomi da suke nuna cewa bidiyon ba daga kasar Afirka ta Kudu ya fito ba.

Misali akwai wasu alluna a gaban shagunan da ke benen wadanda sakon da aka rubuta babu wanda aka yi shi da manyan harsuna 11 da ake amfani da su a kasar.

Kuma mutanen da suka taru a gaban benen galibinsu 'yan kasashen nahiyar Asiya ne.

An fara wallafa bidiyon ne a watan Mayun shekarar 2019, ba kamar yadda aka yi ikirari ba.

Kuma benen da ke ci da wuta, wata cibiyar horaswa ce da ke jihar Gujarat a kasar Indiya, sannan ya fito ne daga kafar yada labarai ta India Today.

Masana suna ganin labaran bogi irin wadannan suna taimaka wa wajen tunzura mutane.

#BokoHaramChallenge

Yanzu haka 'yan Najeriya da 'yan Afirka ta Kudu na sheke ayarsu a shafin Twitter da maudu'in #BokoHaramChallenge, inda suke yi wa juna tsiya game da labarin cewa Boko Haram za ta kai wa kasar hari.

Da dama daga 'yan Afirka ta Kudun suna yin ba'a cewa su kam ba za su iya ja da Boko Haram ba saboda haka sun tattara kayansu sun fice daga kasar.

'Yan Najeriya kuwa lissafa wasu wurare da abubuwa suke wadanda suke so Boko haram ta kai wa hari, ciki har da wannan matar mai cewa 'one minute remaining' - wacce take yin gargadi idan kudin waya sun rage saura minti daya.

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar ci gaba da samun labaran karya, musamman a lokutan tashe-tashen hankula irin wannan.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.

Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba, amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.

Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita.

Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani.

Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.