Ko kun san illar da rashin cin nama ke haifar wa dan adam?

Vegan foods Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani bincike na nuni da cewar, mutanen da ba su cin nama suna fuskantar barazanar kamuwa da mutuwar barin jiki da alamun karancin kamuwa da cututtukan zuciya.

Binciken ya gano cewa a cikin kowane mutum 1,000, ana samun kasa da mutum 10 masu cin tsirrai kadai da ke kamuwa da ciwon zuciya, idan aka kwatanta da masu cin nama.

Binciken da aka wallafa a mujallar aikin likitoci ta Birtaniya ya kwashe shekara 18 yana yin gwaje-gwaje a kan mutum 48,000.

Sai dai binciken bai iya tantance ko shin abincin da mutanen ke ci ne, ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu ne ke haddasa cututtukan ba.

Masana a fannin abinci mai gina jiki sun ce a duk nau'in abincin da mutum ya zaba wa kansa, cin nau'o'in abinci daban-daban na da matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam.

Me binciken ya kara?

Binciken ya yi sharhi kan alkaluman da gwajin wanda cibiyar bincike ta EPIC-Oxford ta fitar. Gwajin wani babban bincike ne na tsawon lokaci kan lafiya da kuma abinci mai gina jiki.

Rabin mutanen da masu binciken suka yi gwaje-gwajen a kansu daga 1993 zuwa 2001 masu cin nama ne. 16,000 daga cikisu ba sa cin nama da kayayyakin abincin da ake samarwa daga dabbobi. Akwai kuma mutum 7,500 daga cikinsu masu cin kifi.

Yayin gudanar da binciken, masanan sun fara tambayar wadanda aka gudanar da gwaje-gwajen a kansu game da nau'o'in abincin da suke ci a san da aka fara gudanar da binciken. Sannan aka kara tambayar su a 2010.

Binciken ya kuma yi la'akari da tarihin yanayin lafiyar mutanen da aka gudanar da binciken a kansu, da irin aikace-aikacen da suke yi na yau da kullum da kuma batun zukar taba.

A karshen binciken, an samu mutum 2,820 masu fama da ciwon zuciya, mutum 1,072 da suka kamu da mutuwar barin ciki - ciki har da mutum 300 masu fama da zubar jini a kwakwalwa, sakamakon yoyon jijiyoyi, wanda hakan ke sa jini diga a kwakwalwa.

Binciken ya nuna cewa kashi 13 cikin 100 na masu cin kifi, ba su fuskantar yawaitar barazanar kamuwa da ciwon zuciya sosai, idan aka kwatanta su da masu cin nama. Kashi 22 cikin 100 na mutanen da ba su cin nama kuma na da karancin yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya,

Sai dai masu cin kayan abinci na tsirrai kadai sun fi fuskantar barazanar kamuwa da mutuwar barin jiki da kashi 20 cikin 100.

Masu binciken na ganin hakan na da nasaba da karancin sinadarin vitamin B12. Amma sun ce akwai bukatar a kara gudanar da bincike domin sanin ainihin alakar da ke tsakanin mutuwar barin jiki da da cin tsirrai.

Akwai yiwuwar babu wata dangantaka tsakanin cututtukan da irin abincin da mutanen ke ci. Yana kuma iya bayyana wasu bambance-bambance a yanayin rayuwar mutane marasa cin nama.

Shin abincin marasa cin nama lafiyayye ne?

Dokta Frankie Philips daga hukumar kula da abinci mai gina jiki na Birtaniya ta ce ba haka ba ne - domin wannan bincike fahimta ce kawai.

"Sun lura tare da bibiyar abincin da mutanen suka ci na tsawon shekaru. Don haka wannan batu ne na dangantaka, ba na tabbatar da sanadi da irin sakamakon da yake haifarwa ba.

"Abin da binciken ke nunawa shi ne yana da kyau mutane su tsara yanayin cimarsu da kyau kuma su rika cin nau'o'in abinci da dama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abinci iri-iri, ba "nama da dankali a kowane dare ba"

"Ba lallai ba ne maciya nama na da wani abinci na musamman ba. Domin za ta iya yiwuwa nama da dankali suke ci a kowane dare, amma ba tare da sun hada da ganyayyaki ba."

Shin abincin da mutanen ke ci ya sauya bayan binciken?

Masu bincike sun kara tambayar mutanen da aka gudanar da gwaje-gwajen a kansu a 2010 game da yanayin abincin da suke ci?

Amma Dokta Phillips ta ce akwai yiwuwar tsarin cimar marasa cin nama da kayayyakin dabbobi sun sauya.

"An tattara wadannan alkaluma ne a cikin gomman shekarun da suka gabata.

"Ta yiwu tsantsar abincin marasa cin nama da kayayin nama na yanzu ya sha banban da yadda yake a shekara 20 ko 30 da suka wuce.

"Nau'o'in abincin marasa cin nama sun karu da yawan gaske.

Kuma mun kara sanin karin wasu barazanar lafiya masu alaka da yawan cin jan nama da aka sarrafa, wanda ke kara yiwuwar kamuwa da cutar kansar hanji.

Me ya kamata in rika ci?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jadawalin abinci mai gina jiki da hukumar NHS ta fitar ya tsara yadda mutum zai daidaita abinci mai cikakken lafiya gwargwadon bukatarsa.

  • Cin kashi biyar na 'ya'yan itatuwa ko ganyayyaki a kullum.
  • Cin abinci mai sunadarin fibre ko gari irinsu dankali, burodi, shinkafa ko taliya.
  • Kar a manta da sunadaren gina jiki.
  • Hadawa da kayan madara.
  • Rage cin abinci mai kitse da sunadarin suga ko gishiri.

Mutanen da ba su cin nama na bukatar su ba da muhimmaci wajen cin isasshen adadin wasu sunadarai.

Misali, mutane da ke cin nama da kayan madara da kifi kan samu isasshen adadin vitamin B12, domin samun lafiyayyen jini da aikin kwakwalwa.

Duk da haka, mutanen da ba su cin kayan dabbobi na iya samun karancin sunadarai a jikinsu, duk da cewar ana sanya sunadarin vitamin B12 a cikin kayan karin kumallo na gwangwani.

Sunadarin Iron ba ya saurin narkewa a cikin kayakin abinci na tsirrai, don haka wadanda suka zabi cewa ba za su ci nama ba, ana bukatar su tabbatar da cewa suna hada abincin da abubuwa kamar fulawa da busassun 'ya'yan itatuwa da sauransu.

A watan Agustan wannan shekarar, an yi wani kira ga mutanen da ba su cin kayan dabbobi da su fahimci bukatar da suke da ita ta su tabbatar da suna cin abinci masu isassun sunadarai da ake kira choline, mai muhimmanci ga lafiyar kwakwalwa.

Labarai masu alaka