Za a dauki hoton ramin black hole daga duniyar taurari

Black hole Hakkin mallakar hoto EHT Collaboration
Image caption A farkon shekarar nan ne masu bincike suka wallafa hoton Black Hole na farko da aka dauka

Masana kimiyyar da suka dauki hoton Black Hole a farko sun bayyana aniyarsu ta daukar sabon hoton na bidiyo ramin daga tsakiyar duniyar taurari.

Sun bayyana cewa za su harba tauraron dan adam da zai taimaka wa kamarorinsu takwas wajen daukar hoton bidiyon.

Masu binciken sun ce sun kara inganta abin hangen nesan da za su yi amfani da shi wajen daukar hoton da yadda za a iya ganin yadda black hole din zai iya hadiye abubuwan da ke gefensa.

Masu binciken da suka gano ramin Black Hole an ba su lambar yabo ta karramawa ta ilimin Physics.

Farfesa Heino Falcke na Jami'ar Radboud da ke Netherland, shi ne ya bada shawarar amfani da ''Event Horizon Telescope,'' wanda shi ne tabarau na hangen nesan da zai taimaka wajen yin bidiyon.

Ya shaida wa BBC cewa mataki na gaba shi ne ganin ramin Black Hole a bidiyo ba wai a tsaye cik a hoto ba.

Ya bayyana cewa kamar yadda duniya ke juyawa, shi ma ramin Black Hole na juyawa, kuma saboda nauyin da ke tattare da ramin, yana kawo cikas ga lokaci da kuma sararin da ke kusa da ramin.

Hakkin mallakar hoto EHT
Image caption Farfesa Heino Falcke

Babban abin wahala shi ne daukar hoto mai kala na irin wannan ramin na Black Hole.

A farkon shekarar nan, masu binciken sun wallafa hoton ramin black hole din da suka dauka a tsakiyar duniyar taurari da aka kimanta da kusan kilomita biliyan 40, girman duniyar da muke ciki sau uku kenan.

Hoton ya nuna iskar gas mai zafin gaske na shiga cikin ramin a launin ruwan lemo.

Hakkin mallakar hoto Katie Bouman
Image caption Dakta Katie Bouman na daga cikin malaman kimiyyar da ta fito da hanyar tattara bayanan da aka samu daga Farfesa Event Horizon Telescope.

Shi dai ramin Black Hole bai da wani launi, amma abin da masu ilimin taurari ke iya gani shi ne yadda wani iskar gas mai zafi ke kwarara cikin ramin.

Iskar gas din na sauya launi idan ta dumfari shiga ramin, tamkar rana idan za ta fadi da yamma cikin gajimare.

Wasu kamfanoni na da niyyar kara abin hangen nesa na girke da za a ajiye a Greenland da kuma Faransa da wasu sassa na Afirka, inda suka nemi tallafi daga wata kungiya a Amurka da ke taimakawa wajen bunkasa kimiyya.

Sun bukaci kungiyar da ta kara tauraron dan adam uku da za su taimaka wa aikin da ake yi a kasa da abin hangen nesa.

Farfesa Falcke ya bayyana cewa wannan zai samar da abin hangen nesa ingantacce kuma na daban, wanda zai iya daukar hoton ramin Black Hole daga tsakiyar duniyarmu.

Labarai masu alaka