Iran na 'amfani da sabbin na'urorin inganta sinadarin uranium'

Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasashen turan da ke cikin yarjejeniyar nukiliya za su iya ceto wannan yarjejeniyar daga rugujewa baki daya

Iran ta bayyana cewa ta fara amfani da sabuwar na'ura domin kara inganta sinadarin uranium dinta, a wani mataki na kara bujera wa yarjejeniyar da aka yi da kasar a 2015 kan nukiliya tare da manyan kasashen duniya.

Iran din na amfani da irin wannan samfarin nau'rar kusan guda 40, kamar yadda mai magana da yawun hukumar da ke kula da harkar nukiliya ta Iran ya bayyana.

Za a iya amfani da sinadarin uranium din da aka inganta wajen hada irin man da ake amfani da shi wajen samar da makamin nukiliya.

Iran dai ta fara watsi da yarjejeniyar da aka yi da ita a watan Yuli bayan da Amurka ta kakaba mata takunkumi.

Shugaban Amurka Donald Trump na son tilasta wa Iran sa hannu a wata sabuwar yarjejeniya da zai dakatar da kasar daga shirye-shiryenta na nukiliya da kuma dakatar da ita daga inganta makamai masu linzami. Amma dai Iran ta ki amincewa da hakan.

Sauran kasashen da ke cikin wannan yarjejeniya sun hada da Birtaniya da Faransa da China da Rasha.

Wadannan kasashen sun yi iya kokarinsu wajen ganin cewa wannan yarjejeniyar ta dore amma takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran ya janyo yawan man da Iran din ke fitarwa ya ragu matuka.

Haka zalika darajar kudin kasar ta yi warwas, farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi a kasar.

Me Iran ta yi dangane da haka?

Hakkin mallakar hoto EPA

Mai magana da yawun hukumar da ke kula da harkokin nukiliya ta Iran din Mista Behruz Kamalvandi ya bayyana sabbin matakan da kasar za ta dauka a ranar Asabar.

Ya shaida wa taron manema labarai cewa hukumar ta samar da na'urar sarrafa sinadarin uranium samfarin ''20 IR-4 da 20 IR-6. Wacce za ta iya sarrafa sinadarin zuwa mafi inganci.

Ya bayyana cewa samfarin na'urar za ta sarrafa sinadarin zuwa adadin abin da kasar ke bukata.

Ya ce kasar za ta iya dakatar da matakan da take dauka a halin yanzu, da sharadin idan sauran kasashen za su koma ga alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar.

Kungiyar da ke sa ido kan nukiliya ta duniya ta tabbatar cewa Iran ta saba yarjejeniyar da aka yi da ita inda kasar ke inganta sama da kilogram 300 na sinadarin uranium.

Labarai masu alaka