An zargi sojin Najeriya da tsare kananan yara

Boko Haram Insurgency Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kare hakkin dan adam ta duniya Human Rights Watch ta zargi sojojin Najeriya da tsare dubun kananan yara ba bisa ka'ida ba, sakamakon zargin suna da alaka da mayakan Boko Haram.

Wani rahoto da kungiyar ta fitar ta ce an tsare yara da dama ba tare da an yanke musu hukunci ba, kuma sun dauki tsawon lokaci suna hannun rundunar sojin.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin kuma rundunar sojin kasar ta ce rahoto ba dai-dai ba ne.

Rundunar ta ce ba ta daukar yaran a matsayin "masu laifi illa a matsayin wanda yaki ya shafi rayuwarsu."

Ta ce duk da cewa tana tsare mata da yara da suke ganin kungiyar Boko Haram ta sauya wa tunani, "ana ciyar da yaran yadda ya kamata kuma ana sauya masu tunaninsu kafin a sake su."

Kuma alamu sun nuna cewa an jibe yaran ne a barikin sojoji, ba tare da an basu damar ganawa da iyalai ko abokan su ba.

Rahoton kungiyar mai shafi 50 wanda aka yi wa taken "Babu wanda ya san ina mace ko raye" ya mayar da hankali ne kan yadda sojoji suka tsare kananan yaran da ake zargi suna da alaka da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ta ce barin yaran da yunwa, duka, tsananin zafin da su ke fama da shi baya ga cunkoson wuraren kwana da suke ciki na nuna cewa ana cin zarafinsu sosai.

Human Rights Watch ta ce an dauki tsawon shekaru ana tsare kananan yaran da ba su ji ba, ba su gani ba, kuma babu wata cikakkiyar hujjar da zata bayyana cewa suna da alaka da mayakan na boko haram.

Kuma har yanzu babu wanda aka mika gaban kotu.

Da dama daga cikin wadandan yaran sun fuskanci ibtila'in Boko Haram, inda suka sha da kyar daga hannun mayakan.

"Sai dai cin zarafin da hukumomin kasaer ke musu ba komai yake janyowa ba face kara sanya su a wani halin ni 'ya su," a cewar daraktan sashen kare hakkin kananan yara Jo Becker

Kungiyar ta ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta sanya hannu tare da aiwatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na mika kananan yaran da ke tsare a hannun sojoji ga hukumomin kare hakkin kananan yara, domin gyara musu hali.

Akwai bukatar a mayar da kananan yaran hannun danginsu domin su ci gaba da mu'amala da sauran al'umma.

Sauran kasashen da ke fama da yake-yake da suka hada da Chadi, Mali da Jamhuriyar Nijar tuni suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da dama daga cikin kananan yara da aka kama an tsare su ne a barikin sojoji na Giwa da ke birnin Maidugurin jihar Borno a arewa maso gabashin kasar

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa tsakanin watan Janairun 2013 zuwa Maris din 2019 sama da kananan yara 3,600 sojojin Najeriya suka tsare kuma sun hada da mata 1,617 sakamakon zargin su da alaka da masu rike da makamai.

Da dama daga cikin kananan yara da aka kama an tsare su ne a barikin sojoji na Giwa da ke birnin Maidugurin jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A watan yuni 2019, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi hira da wasu kananan yara 32, wadanda aka taba tsarewa a barikin Giwa sakamakon zargin su da alaka da Boko haram.

Babu wani daga cikin yaran da ya bayyana cewa an gurfanar da su gaban wani alkali ko kuma kotu, kamar yadda dokar kaar tace.

Guda daga cikin yaran ya bayyana cewa mutum guda ya taba gani da ya yi tsammanin wani lauya ne, babu wanda ya san takamaiman tuhumar da ake masa.

Daya daga cikin su ya kuma bayyana cewa sojojin sun tsare shi ne tun yana dan shekaru biyar da haihuwa.

Mahukuntan Najeriya sun kama kananan yaran ne yayin gudanar da ayyukan tsaro na soji, tantance 'yan gudun hijira, da kuma samun labarai daga masu kwarmato bayanai.

Da dama daga cikin yaran sun ce an cafke su ne lokacin da suke tsere wa rikicin mayakan Boko Haram daga kauyukan su ko kuma yayin neman mafaka a sansanonin 'yan gudun hijira.

Wani daga cikin kananan yaran ya bayyana cewa an cafke tare da tsare shi har tsawon shekaru biyu, sakamakon zargin cewa yana sayar da "Doya" ga mayakan Boko Haram din.

Hakkin mallakar hoto John Homes for Human Rights Watch

Kananan yara mata da dama ne mayakan suka sace tare da tilasta musu cigaba da zama da su a matsayin matan su.

Da dama daga cikin kananan yaran da Human Right Watch ta tattauna da su, sun shaida mata cewa sun ga gawarwakin wasu daga cikin wadanda aka tsare a barikin soji na Giwa da ke birnin Maiduguri.

Da dama daga cikinsu sunce sun fuskanci matsananciyar yunwa da kishirwa lokacin da suke tsare.

Tun a watan Janairun 2013, hukumomin Najeriya suka saki akalla yara 2,200 , kuma an sako su ne ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi da ke da alaka da kungiyar Boko Haram ba.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, an tsare yara 418 a shekarar 2018.