Me ya sa Satumba ne sabuwar shekarar makarantu?

Children putting their hands up to answer questions in a classroom Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ku daga hannunku idan kun san dalilin da ya sa sabuwar shekarar makaranta ke farawa a Satumba

Mafi yawan yara a sassan duniya daban-daban sun koma makaranta a wannan makon, yayin da wasu kuma za su koma a mako mai zuwa, wasu yaran ma ranarsu ta farko ke nan a aji.

To ko me ya sa sabuwar shekarar makaranta ke farawa a watan Satumba?

Bari mu yi maza mu duba tarihi.

A Birtaniya, zuwa makaranta bai zama wajibi a kan yara ba sai a shekarar 1880, kuma a lokacin yara na aiki ne a gonaki da kamfanoni kamar iyayensu.

Wata 'yar kungiyar masana tarihi Paula Kitching ta ce an sanya farawar sabuwar shekarar makarantu ne a daidai lokacin da aikace-aikace ke yawa kamar na noma da ayyukan masana'antu a kasar Ingila.

Ta ce "A lokacin hunturu babu aikin yi sosai, don haka idan yara suka yi fashin zuwa makaranta ba laifi ba ne."

Amma daga karshen watan Mayu zuwa sama, ana tsammanin kowa ya ci gaba da aikace-aikacen gona irinsu tsinkar kayan marmari, kulawa da dabbobi, girbewa da kuma adana amfanin gona.

"A al'ummomi da yawa, yara maza 'yan shekara 10 zuwa 13 ne ke kiwo a filayen kiwo a domin haka za su kasance ba su je makaranta ba na tsawon kwanaki."

Ta kara da cewa, kananan yara za su taimaka wajen kulawa da gida da kannensu da kuma wanki sai manyan yaran su taimaka wa iyaye wajen sauran ayyuka.

"A domin haka a lokacin bazara lokacin da ake kammala irin wadannan ayyuka, akwai lokacin da yara za su je makaranta," a cewarta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A zamanin yanzu kuwa sai yara sun kai shekara 13 kafin a ba su damar yin aiki a bisa tsari

Stephanie Spencer, daya daga cikin masana kungiyar tarihin ilimi ta ce ana fara karatu a watan Satumba ne domin samun karin yawan yara da ke shiga makarantu.

Dokar ilimi ta shekarar 1880 ta bayyana cewa dukkan yara masu shekara biyar zuwa 10 sai sun je makaranta.

A cewar wata takarda ta 'yan majalisa, an samu matsalar kin zuwa makaranta ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a farkon shekarar 1890, kuma an samu raguwar masu zuwa makarantar da kashi 82 cikin 100.

Takaddar ta nuna cewa an yi kiyasin yara 300,000 ne ke aiki a waje a sa'o'in da ake a makaranta.

Mis Spencer ta ce yayin da iyaye ke kokarin biyan kudin makaranta na yaran kafin dokar ta canja a shekarar 1891, iyaye na batar da kudin da ake biyan yaran na aikin da suka yi har ma da kari.

"Magana ce ta sa iyaye su kai yaransu makaranta kuma gwamnati ta sani cewa iyayen ba su da yadda za su yi su saka su a makarantu a lokacin yanayi na zafi."

Wannan labarin na da nasaba da tambayar da Mark Moore ya yi daga Cheschire inda ya yi tambaya cewa: "Me ya sa makarantu ke farawa a watan Satumba?"

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba