Najeriya: Me ya sa har yanzu ba a biyan haraji?

Lagos oil platforms Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Oil has been a major revenue source

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa kasar na iya shiga matsalar karancin kudi muddin ba a ingantan hanyoyin karbar haraji a kasar ba.

Kasar ta kasa cimma burinta na tattara kudaden shiga da kimanin kashi 45 cikin 100, yayin da kudaden da gwamnatin Najeriya ke kashewa suka ninku kuma kudaden da kasar ke kashewa wajen biyan bashi suka karu.

Duk da haka fadar shugaban kasar ta yaba kokarin da hukumar karbar harajin kasar (FIRS), wurin rubanya kudaden shigan gwamnati tun daga shekarar 2015.

Jama'a a shafukan abota na ganin akwai alamar tambaya a kan hakan. Suna cewa idan har da gaske ne, to ya aka yi ba a samu karuwar kudaden shiga ba, wanda gwamnati za ta yi amfani da su wurin inganta hanyoyi da bangaren ilimi da lafiya.

Karin masu biyan haraji

Alkaluman da gwamnatin kasar ta fitar sun nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 19 suka biya gwamnati haraji a shekarar 2018.

Wani rahoton bankin duniya ya nuna cewa an samu karuwar 'yan Najeriya da ya kamata su rika biyan haraji a kasar zuwa kashi 65 a shekarar 2018.

Amma duk da haka kasa da kashi 35 cikin 100 na jama'ar ne ke biyan harajinsu.

Gwamantin kasar na bibiyar attajiran kasar domin karbar harajin da ta ke ganin suna kin biya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shekara biyu da suka wuce, gwamnatin ta ba wa attajiran wa'adin watanni goma sha biyu su bayyana kadarorinsu da kudaden shigarsu, sannan su biya bashin harajin da ta ke bin su a kai domin guje wa biyan tara ko hukunci a gaban kotu.

Bankin Duniya, a rahotonsa na 2018 ya ce duk da rangwamen da gwmantin ta yi, a karshen watan kashi 18 na attajiran da aka nufa da tsarin ne suka ba da hadin kai.

Akwai yiwuwar wasu 'yan Najeriya ba su da kwarin gwiwar biyan harajinsu saboda zargin ana iya karkartar da kudaden, maimakon a yi amfani da su wurin bunkasa bangaren lafiya, ilimi da samar da abubuwan more rayuwa.

Faduwar farashin mai

Manyan matsalolin da gwamnatin ta samu su ne faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma karyewar tattalin kasar a 2016.

Farashin gangar danyen mai ya yi mummunar faduwa daga Dala 113 a shekarar 2012 zuwa Dala 54 a shekarar 2017.

Najeriya, wacce ita ce kasa mafi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka na samun kashi 75 na kudaden shiganta daga bangaren mai a shekarar 2012 zuwa 2014. Amma daga shekarar 2016 zuwa 2018 sai Kudaden shigar suka ragu zuwa kashi 41.

Gwamnatin kasar ta ce tun a shekarar 2015 harajin kamfanoni da wanda ake cirewa a kan kayayyakin da mutane ke saye wato VAT na ta karuwa.

Amma wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na 2019 ya bayyan cewa gibin da aka samu wurin tara kudaden shigar kasar a 2018 na daga cikin mafiya girma da aka samu a nahiyar Afirka.

VAT gap in selected African countries

Assumes all private consumption would have paid VAT
Source: UN Economic Commission for Africa

Hukumomin kasar su ce daga cikin matakan da kasar ke bi don fadada hanoyinta na samun haraji daga watan Janairun 2020 za ta fara karbar haraji a kan kayan da ake saye ta intanet a cikin gida da kasashen waje.

Rahoton da cibiyar Oxford Martin School da ke jami'ar Oxford ta fifar ya kiyasta cewa kudaden shigan Najeriya a bangaren da ba na man fetur ba sun karu. Amma hauhawar farashin kaya da faduwar darajar kudin kasar sun kawo koma baya.

Matsayin tattalin arzikin a duniya

Wasu alkaluman na kiyasta cewa Najeriya ce kasar da ke karbar haraji mafi karanci daga kayayyaki da aikace-aikacen da ake samarwa a cikin gida.

Kungiyar da ke sanya ido kan cigaban tattalin arziki (OECD), mai auna karfin arziki manyan kasashe ta ce, kashi shida cikin 100 ne harajin da Najeriya ta samu daga kayayyaki da aikace-aikacen cikin gida a shekarar 2016.

Alkaluman da da rahoton hukumar ya fitar a kan 2016 su ne mafi sabunta a halin yanzu.

Rahoton kungiyar ya nuwa cewa Afirka ta Kudu na samun kashi 29 cikin 100 a matsayin harajin kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, a Ghana kashi 18, Masar 15, a Kenya kashi 18.

Matsakaicin adadin da OECD ta sanya shi ne kashi 34 cikin 100, har a kan manyan kasashe masu karfin tattalin arziki.

Ma'aunin da bankin duniya ke amfani da shi wurin auna yanayin karbar haraji, wanda ya hada da biya kudaden kula da 'yan kasa, ya bambanta.

Karancin harajin da Najeriya ke samu

Bayanai: Bayanan OECD na 2016

Mizanin bankin duniyar ya ce kasa da maki 3.4 ne harajin da Najeriya ke karba daga kayayakin da ake samarwa a cikin gida.

Adadin ya karu zuwa kashi 4.8 cikin 100 a 2017 kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Ba mu da alkaluman 2018 ba, amma yana da kyau mu yi bayani cewa bankin duniya ya ce akwai matukar muhimmanci ya samu maki 15 cikin 100 domin kawo cigaban tattalin arziki da rage talauci.

Ya ake bunkasa karbar haraji?

Yawan harajin da wasu kasashe masu tasowa ke karba kan kayan da ake samarwa na cikin gida ba yawa.

Alkalumwan da aka samu a kasashe kusan 60 na nuna cewa adadin bai fi kashi 15 cikin 100 ba.

Wani mataimakin darektan asusun ba da lamuni na duniya IMF, Bernardin Akitoby, ya ce kasashen da suka ci gaba na karbar harajin kusan kashi 40 cikin 100.

Ya ce mizanin na karbar haraji ya bambanta daga kasa zuwa kasa, kuma akwai darussa da za a iya dauka daga wasu kasashe da suka yi nasara a baya a wannan bangare:

  • Dora nauyi kai tsaye don magance matsalar karancin biyan haraji
  • Tsarin karbar haraji masu sauki da kuma rage adadin da ake karba da wadanda ake tsamewa
  • Sanya haraji a kan hajojin da ake saye da sayarwa
  • Bunkasa karbar kudaden shiga ta hanyar amfani da fasahar zamani

Labarai masu alaka