Shiites: 'An kashe mana mambobi 15 – IMN

'Yan Shi'a masu zanga-zanga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar IMN ta ce an kashe mambobinta da dama

Kungiyar IMN ta 'yan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta ce jami'an 'yan sanda a Najeriya sun kashe mambobinta 15 yayin da suke tattakin ranar Ashura a ranar Talata.

Mai magana da yawun kungiyar, wadda gwamnati ta haramta, Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa an kashe mutum shida a jihar Bauchi, sannan kuma aka kashe uku a jihar Kaduna.

Sauran sun hada da mutum biyu da aka kashe a Sokoto da kuma uku a Gombe, sai kuma mutum daya a Malumfashin jihar Katsina.

Sai dai rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta musanta ikirarin, amma mai magana da yawunta Yakubu Sabo ya bayyana wa BBC cewa sun tarwatsa masu tattakin da aka haramta.

Amma an kammala tattakin cikin kwanciyar hankali a jihohin Kano da Filato da kuma birnin Abuja, in ji Ibrahim Musa.

Ya kuma kara da cewa yawan wadanda suka rasu din ka iya karuwa.

Tun farko dai rundunar ta ce haramcin yin tattakin iya 'yan kungiyar IMN ya shafa ba duka Musulmi ba a Najeriya.

"Biyo bayan neman karin bayani da mutane ke yi kan haramta kungiyar IMN, ya zama wajibi a sani cewa haramcin yin tattakin ya shafi 'ya'yan kungiyar IMN din ne kawai.

"Saboda haka sauran al'ummar Musulmi da suke da sha'awar yin tattakin Ashura a fadin Najeriya za su iya bin sahun sauran Musulmin duniya domin yin haka."

Kungiyar ta IMN ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Twitter mai suna @SZakzakyOffice, inda ta ce su ne na mutanen da jami'an tsaron suka harbe mata.

Ranar Talata ce 10 ga watan Muharram da 'yan shi'a suke yin tattakin Ranar Ashura da aka kashe jikan Manzon Allah SAW, Imam Hussaini dan Aliyu dan Abi Talib.

Mabiya Shi'a a duniya na gudanar da jerin gwanon domin nuna bakin cikinsu da kisan na Imam Hussaini ibn Ali, a yakin Karbala.

Labarai masu alaka