Yadda za a shawo kan mai tunanin kashe kansa

A younger man and his elderly father (stock picture) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Vulnerable social groups are particularly at risk for suicide

A kowane dakika 40 mutum daya na rasa ransa ta hanyar kashe kansa a fadin duniya.

Kusan mutum 800,000 ne ke rasa ransu ta hanyar kashe kansu da kansu duk shekara, a cewar raoton Hukumar lafiya ta Duniya (WHO), kisan kai da kai ita ce babbar hanyar mutuwa ta biyu tsakanin 'yan shekara 15 zuwa 29 bayan hatsarin ababen hawa.

Akwai bayanai masu tsorartarwa sosai game da ita wannan matsala, amma duk da haka WHO ta ce ba kasafai ake tattauan ta ba.

Duk yadda abin ya kai, a karshe dai wadanda abin ya fi shafa su ne yara da 'yan uwa da abokan zama da abokai da kuma abokan aikin wanda ya kashe kan nasa.

Wani rahoton kasar Amurka da aka wallafa, ya ce duk sadda wani ya kashe kansa abin kan shafi wasu mutum 135.

Dakta Julie Cerel na University of Kentucky ya gano cewa tasirin kisan kai da kai yana kara girma ne ga mutane bisa yadda suka fi jin kusancinsu da mamacin, ba lallai sai ya kasance dan uwansu na jini ba.

Amma a wasu lokuta mukan fuskanci kalubalen tattaunawa kan wannan matsala mai girman gaske.

Yayin bikin ranar yaki da kisan kai da kai ta duniya, mun duba wasu abubuwa da za ku iya yi domin tattauna lamarin tsakanin al'umma da nufin dakile matsalar.

Fara tattaunawar

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption WHO ta ce yana da amfani sosai a rika taimaka wa kananan yara wajen yaki da kalubalen rayuwa

Babu wata takamammiyar hanyar tattaunawa kan kisan kai da kai - fara tattauawar shi ne abu mafi muhimmanci, in ji Emma Carrington, wata mai magana da yawun Rethink UK a hirarta da BBC.

"Ya kamata mu fahimci cewa magana ce mai nauyi, ba irin wadda muka saba yi ba ce kullum. Sabooda haka za ka ji tsoro yayin hakan amma babu wata matsala.

"Matsalar ta riga ta kai halin lahaula, abin yi shi ne kawai ka saurari mutum ba tare da ka yanke masa hukunci ba."

Shawarwari kan yadda za ka shawo kan mai tunanin kashe kansa:

 • Zabi wurin da babu hayaniya, inda mutumin yake da nutsuwa.
 • Tabbata kuna da isasshen lokacin tattaunawa.
 • Idan kun fadi wani abin assha kada ku firgita, kada ku matsa wa kanku.
 • Daukar hankalin mutumin, rika kallon idonsa, ajiye wayarka a gefe, ba shi cikakken hankalinka.
 • Ka yi hakuri da shi, zai iya daukar lokaci kafin ya bayyana abin da ke damunsa.
 • Ka yi amfani da budaddun tambayoyi wadanda ke bukatar amsa sama da "eh ko a'a".
 • Kada ka katse shi ko ka kawo mafita: kada ka nuna cewa ka san yadda mutumin yake ji a ransa.
 • Ka bincika ko ya san inda zai samu taimakon likitoci.

Wa ke cikin hadari?

Kisan kai da kai ya shafi kowanne aji na mutane amma maza sun fi aikata shi.

Kiyasin kisan kai da kai tsakanin maza ya kai 13.5 cikin mutum 100,000 a 2016 idan aka kwatanta da na mata a 7.7 cikin mata 100,000.

Sai da yawan masu aikata hakan tsakanin maza da mata ya bambanta tsakanin kasashen duniya.

Kasar rasha ce ke da mafi yawan maza - 48 cikin mutum 100,000 a 2016 - ninki shida kenan na yawan abin tsakanin mata.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ko da ba ka yarda da abin da mutumin ke fada ba, ya kamata ka kyale shi ya bayyana abin da ke damunsa

"Wani lokacin mutum kan ji kadaici ko da kuwa yana kewaye da jama'a. Wasu kan kasance cikin kangin talauci. Duk wadannan ka iya taruwa a kan mutum," in ji dakta Carrington.

"In dai ba a taimaka wa irin wadannan mutane ba, to abu zai masu yawa."

Me al'umma za ta iya yi?

WHO ta ce akwai abubuwa da dama da gwamnatoci za su iya yi domin dakile kisan kai da kai:

 • A yi kokarin fara tattauana matsalar.
 • Taimaka wa kananan yara yin yaki da kaluabalen rayuwa, musamman a makarantu.
 • Horar da ma'aikatan lafiya domin su gane take-taken aikata kisan kai da kai.
 • Tantancewa tare da taimaka wa mutanen da ke cikin hadari da kuma ci gaba da tuntubarsu .
 • A takaita damar da mutane ke da ita ta amfani da abubuwa masu saurin kisa.

Dakile jita-jita

Kungiyoyi masu yaki da cututtukan da suka shafi kwakwalwa sun ce suna yaki da jita-jita kan kisan kai da kai: tattaunawa da mai tunanin kashe kansa za ta ingiza shi ne kawai.

Amma wata kungiya mai kula da walawala mai suna Beyond Blue, wadda kuma tsohuwar firaministar Australia Julia Gillard ke jagoranta, ta ce tattaunawar za ta bai wa mai wannan tunanin kwarin gwiwa ne.

"Ba lalle sai ka zama kwararre a bangaren lafiya ba sannan za ka iya agaza wa wanda ke shirin ingiza kansa lahira. Kawai ana son ka zama cikin shirin tattaunawa da wanda yake cikin wannan hali, a cewar Gillard yayin da take gabatar da sakamakon binciken.

Yayin da samun taimakon kwararru ita ce hanyar sauki zuwa ga samun magani da kulawa, Carrigton ta ce fitowa karara a yi magana a kan kisan kai da kai zai nuna cewa ba ka yi saurin yanke hukunci ba.

Sannan hakan zai taimaka masu wajen samun nutsuwa na dan lokaci.

''Watakila za su ce 'kash, ba kisan kai nake tunani ba kuma shi ne karshen zancen. Sai dai a wajen akasarin mutane, a lokacin da ba sa jin dadi, wata zuciyar za ta rika ayyana masu aikata kisan.''