Trump ya kori mai ba shi shawara kan tsaro

John Bolton Hakkin mallakar hoto EPA

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kori mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro John Bolton.

Trump ya rubuta cewa, ya sanar da John Bolton a jiya da daddare cewar ba a bukatar ayyukan shi a Fadar White House.

Shugaba Trump ya ce bai yi na'am da shawarwarin da yake ba shi ba, inda ya kara da cewa, zai nada sabon mai ba shi shawara a mako mai zuwa.

An samu labarin korar Bolton ne yayin da aka samu rarrabuwar kai a tsakanin mambobin majalisar shi akan soke tattaunawar da za a yi da Taliban da aka gayyata zuwa Amurka.

Mista Bolton ne mutum na uku daya rike wannan mukamin a gwamnatin Trump, tun Afrilun shekarar 2018, bayan Michael Flynn da kuma HR McMaster.

Sakatariyar yada labarai Stephanie Grisham ta fada wa manema labarai cewa "Bolton da Trump sun sha bamban kan tsare-tsare da dama. "

A na shi bangaren, Mista Bolton ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, ya rubuta takardar barin aiki a daren Litinin din da ta gabata.

A cewar Fadar White House, Mista Bolton ya shirya wata tattaunawa da 'yan jarida a fadar White House ne tare da Sakataren Harkokin Waje, Mike Pompeo da kuma Sakataren Baitul Mali, Steven Mnuchin sa'o'i biyu kafin hakan ne aka samu labarin cewa Trump ya sallame shi.

Majiya da dama sun bayyana cewa majalisar tsaro ta kasar wanda ke bai wa shugaban shawara, ta zama saniyar ware a fadar White House karkashin jagorancin Bolton.

Labarai masu alaka