Kotu na yanke hukunci a shari'ar Buhari da Atiku

Atiku na kalubalantar zaben Buhari Hakkin mallakar hoto NURPHOTO
Image caption Lokacin da Atiku da Buhari ke dasawa

Ranar Laraba kotun sauraron kararrakin zabe ke yanke hukunci a kan karar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya shigar a gabanta ta kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

Atiku Abubakar ya shigar da karar ne bayan da hukumar zaben kasar INEC ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya ci zaben ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2019.

Tun a baya lauyan da yake kare hukumar INEC Yunus Ustaz (SAN) ya ce hukumar ta bi duka ka'idojin da doka ta shimfida wajen gudanar da zaben, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika a wani zaman kotun na baya, lauyan da ke kare Shugaba Buhari Wole Olanipekun (SAN) ya bukaci da kotun ta yi watsi da karar "saboda rashin kwararan hujjoji." kamar yadda ya ce.

Shi ma a nasa bangaren lauyan jam'iyyar APC Lateef Fagbemi (SAN) ya ce jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar sun yi zargin saba ka'idojin zabe a rumfunan zabe 119,973 a mazabu 8,809, ya gabatar da shaidu 62 kuma hujjoji biyar kacal suka gabatar daga cikin rumfunan zaben.

Sai dai lauyan PDP da kuma Atiku Abubakar, Levy Uzoukwu (SAN) ya bukaci kotun da ta yi amfani da sashi na 138(1) na dokar zabe, inda dokar ta bukaci soke takarar duk wanda ya gabatar da bayanan karya.

Lauyan PDP ya ce Shugaba Buhari ya kasa gabatar da shaidar wasu makarantu da ya ce ya halarce su a fom din da ya mika wa hukumar INEC.

Yanzu dai kallo ya koma wajen alkalan kotun sauraron kararrakin zaben, wadanda za su yanke hukunci a zaman kotun na yau Laraba.