Me ya sa Buhari ya amince a kara haraji kan kayayyaki?

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto BUHARI SALLAU

Gwamnatin Najeriya ta amince a kara haraji kan kayayyaki daga kashi biyar cikin dari zuwa kashi 7.2 cikin dari.

Mininstar kudin kasar, Hajiya Zainab Ahmed, ta shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa an dauki matakin ne lokacin taron majalisar ministoci.

Amma wannan sabon karin haraji ba zai soma aiki ba sai ya samu amincewar 'yan majalisar dokokin kasar.

Idan suka amince da sabon karin, zai soma aiki a shekarar 2020.

Zainab Ahmed ta ce an kara harajin ne domin gwamnati ta samu damar iya biyan albashin da aka kara wa ma'aikata na dubu talatin mafi karanci.

Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Zainab Ahmed ta ce an kara harajin ne domin gwamnati ta samu damar iya biyan albashin da aka kara wa ma'aikata na dubu talatin mafi karanci.

A cewar ta, majalisar ministocin ta bukaci a tattauna da jihohi da kananan hukumomin kasar kan yadda za a tabbatar da karbar Karin harajin kasancewa suna cikin masu morar sa.

Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin marigayi Janar Sani Abatch ce ta fito da sabon tsarin haraji inda ake karbar kashi biyar cikin dari kan kayayyakin da aka saya.

Amma gabanin saukarsa daga kan mulki a shekarar 2003, tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya kara haraji zuwa kashi goma cikin dari.

Sai dai gwamnatin marigari shugaba Umaru Musa 'Yar Adua ya komo da harajin zuwa kashi biyar cikin dari bayan kungiyar kwadago ta bayyana rashin jin dadin ta.