Za a fara sauya wa mata ruwan al'aura

Ba a daukar BV ta hanyar jima'i duk da cewa cuta ce da ke kama kwayoyin halitta. Hakkin mallakar hoto Getty Images

Likitoci a Amurka na fatan fara sauya wa mata ruwan al'aura kuma sun kaddamar da wani shiri don tantance matan da za su iya bayar da ruwansu.

Suna tunanin cewa wasu matan za su amfana da ruwan wanda kwayoyin halittarsa ke da isasshiyar lafiya don kariya daga wata cuta mai suna bacterial vaginosis (BV).

Wata tawaga a Jami'ar Johns Hopkins ta na da karfin gwuiwa kan nasarar da aka samu dalilin sauyin bayan gida ta zaburar da su.

Duk da cewa akwai magungunan da ke warkar da cutar BV, wani lokaci ta kan dawo.

Mece ce cutar BV?

Ba a daukar BV ta hanyar jima'i duk da cewa cuta ce da ke kama kwayoyin halitta.

Ana yawan kamuwa da ita kuma matan da suka kamu da ita za su lura cewa wani irin ruwa mai karni yana fita daga al'aurarsu.

Ba wata cuta ce mai tayar da hankali ba, amma dole ne a magance ta saboda cutar BV na jefa mata cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i da kuma cututtukan mafitsara.

Idan mace na da ciki, cutar BV na iya sa wa ta haifi danta kafin lokacin haihuwar ya yi.

Ta wace hanya sauya ruwan al'aurar zai taimaka?

Ana kamuwa da cutar BV ne idan aka samu sauyi a yanayin a kwayoyin halittar da ke cikin al'aurar mace.

Al'aurar mace, kamar hanji, na dauke da kwayoyin halitta iri-iri.

Abincin da muke ci da yanayin yadda muke gudanar da rayuwar da wasu magunguna da muke sha na iya rikita shirin kwayoyin halittar.

Kwararru sun ce kwayoyin halittar da ke cikin al'aura sun fi son wuri mai zafi, don haka idan yanayin cikin al'aura ya rage zafi sosai, kwayoyin cutar dake janyo cutar BV na yaduwa.

Akwai abubuwan da kan janyo haka, kamar yin jima'i (ruwan maniyyi kan sanyaya cikin al'aura) da amfani da kora ruwa cikin al'aura ko kuma amfani da sabulai na musamman na wanke al'aura da kuma sauyi a sinadaran jikin dan adam musamman a lokacin al'ada.

Ya za a yi sauyin?

Masu binciken na ci gaba da duba abin da ya dace don fara bai wa matan da ke fama da cutar BV damar yin sauyin wanda suke fata su yi kwanan nan tunda sun samu amincewar Hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka.

Sun tantance kadan daga cikin matan da suke so su bayar da ruwan al'aurarsu kuma sun ruwaito cewa bincikensu na mujallar Frontiers in Cellular and Infection Microbiology.

Bisa mata 20 da suka gwada, masu binciken sun ce sun gano wasu abubuwa kan wadanda suka dace su bayar da ruwan al'aurarsu.

Don kada a samu matsala, za a umarci wadanda za su bayar da ruwan al'aurarda su kaurace wa jima'i tsawon a kalla kwana 30 kafin a diba ruwan, kuma za a tantance su don tabbatar da cewa ba su da wata cuta kamar HIV.

Daya daga cikin masu bincike, Dakta Laura Ensign ta ce: " Mace da kanta za ta nemo ruwan da take so a sa mata, mun san kuma mutane sun fi son haka."

Macen za ta sa sannan ta cire wani 'yar kewayayyar roba- wacce take kama da kofin al'ada to debo ruwan.

"Ba ya daukar wani lokaci kuma abu ne mai sauki. Diba daya zai isa a sauya sau daya," a cewarta.

Za a sa shi a cikin wani bututu sai wadda za a sauya ma wa ta zura bututun a cikin al'aurarta sannan ta zuba ruwa.

Dakta Ensign ta ce: "In da za mu sami kudi, za mu iya fara dashen nan da nan. Wasu daga cikin wadanda za su ba da ruwansu da muka duba sun ce suna sha'awar bayarwa. ''

"Muna so mu fara sauya wa mata 40. Sannan za a bai wa dukansu magungunan cutar BV din da suke fama da ita."

Labarai masu alaka